Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta gabatar da kudiri tare da kira ga Gwamnatin Tarayya ta karrama marigayi Ali Kwara, duba da irin gudunmawar da ya ba wa harkar tsaro a kasar nan.
Shugaban Majalisar, Abubakar Y. Suleiman ne ya bayyana haka bayan da dan majalisa mai wakiltar Disina, Saleh Hodi Jibir, ya gabatar da kudurin bukatar a yi wa mamacin addu’a ta musamman tare da karrama shi.
Jibrin ya kara da cewa marigayi Ali Kwara ya taimaka wa harkar tsaro a Najeriya da ma Afrika baki daya, inda ya yi ta yaki da masu aikata laifuka iri-iri.
Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Tijjani Muhammad Aliyu, ya jinjina wa Hodi bisa kawo kudurin, sannan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya a kan ta karrama mamacin.
Daga baya Majalisar ta ware minti biyu domin yiwa marigayin addu’ar samun rahama daga Ubangiji.
Marigayi Alhaji Ali Kwara fitaccen mai kama barayi ne da ya taimaka wajen ruguza ayyukan ‘yan fashi musamman a dazukan da ke yankin Arewacin Najeriya.
Ali Kwara wanda ya shafe shekaru yana kama ‘yan fashi yana mika wa gwamnati domin hukunta su ya rasu ne a ranar Alhamis a Abuja bayan fama da rashin lafiya.