✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Ya kamata gwamnati ta bai wa masu magungunan tsirrai cin gashin kansu’

Kyari Abba Goni ya yi fice wajen zurfafa karatu a ilimin magungunan tsirrai.

M.H Kaka Kyari Abba Goni ko Master Herbalist kamar yadda ake kiran likitocin magungunan tsirrai a Turance, ya yi fice wajen zurfafa karatu a ilimin bangaren, inda ya faro daga Jami’ar Maiduguri kafin ya je Ingila da kuma kasar Sri lanka.

Ya yi wa Aminiya bayani a kan maganin wanda kasashe irin su Sin ke bai wa muhimmanci, da dai sauran batutuwa.

Ko za ka fara da gabatar da kanka?

Sunana Kaka Kyari Abba Goni. Ni haifaffen garin Maiduguri ne; a can na yi makarantar firamare na yi sakandare a garin Damagum a Jihar Yobe.

Bayan nan na je Jami’ar Maiduguri, inda na samu digiri kan ilimin itatuwa wato Botanical.

Na yi project a kan Medicinal Plant da ke taimakawa wajen hada magunguna daga tsirrai.

Sannan na zurfafa karatu a makarantar magungunan gargajiya ta London, wato Herbal Medicine Academy of London, inda na yi karatun shekara 2 ta yanar gizo har na gama.

Na kuma yi karatu a kan Yunana Medicine, wanda tsarin magunguna ne da ya samo asali daga kasar Girka, sannan masana daga duniyar Musulmi suka fadada zuwa matakin da yake yanzu ake kiransa Islamic Medicine.

A 2015 na yanke shawarar bude cibiyar magunguna a garin Maiduguri. Sai dai ba a jima ba sai na samu wani gurbin karatu a kasar Sirilanka a babban Birninsu na Colombo.

Na yi karatun ne kan ilimin magungunan gargajiya na kasar Sin wato Akifoncho, a wata jami’ar ilimin tsirrai da ke birnin.

Na samu takardar M.D a kai, wato Medical Doctor ko likita a wannan bangaren.

Ina rike da matsayin Master Herbalist, matsayi ne a bangaren kamar yadda za ka kira likita da sunan Dokta a bangaren ilimin magungunan Orthodod, wato magungunan zamani na kemis.

Me ya karfafa maka gwiwar bude cibiyar magunguna maimakon aiki a jami’a ko wata ma’aikatar gwamnati?

A lokacin da na je aikin hidimar kasa a Jihar Akwa Ibom, an yi mana lakcoci da horo kan muhimmancin kasancewa mai dogaro da kai ta fuskar sana’a da samar da aikin yi ta hanyar kafa karamar masana’anta wato Entrepreneurship, maimakon jiran a samu aikin gwamnati.

Wannan ya karfafa mani gwiwa kwarai. Akwai kuma wani Farfesa na ilimin itatuwa a Jami’ar Fatakwal da na samu karin karfin gwiwa daga wajensa.

Yana koyarwa a jami’ar, amma sai ya ajiye aiki ya rungumi samar da magungunan tsirrai tare da rungumar harkar dungurugum.

Ko za ka yi mana bayani kan shirin da kake gabatarwa ‘Abincinka Maganinka’ a Sunna TB?

Yana nufin abin da kake ci na iya zama magani a gare ka, kamar yadda kuma zai iya zame maka cuta.

Wannan ya rage ga al’umma su maida hankali sosai wajen tsara irin abincin da za su ci gwagwadon karfinsu.

Allah da kanSa cikin Alkur’ani mai girma ya ce: “Ya ku mutane ku ci daga dadada na abin da na arzuta ku da shi,” wannan bukata ce da ya yi ga daukacin al’umma ba masu imani kadai ba.

Wasu sun fassara dadadan nan, da abinci mai amfani ga jiki (nutrition). Abincin ya rabu kashi-kashi na abin da ake kira mineral a Turance har guda 102, wanda kowannensu yana da amfani ga jikin dan Adam.

Wani jiki na bukatarsa sosai, wani kuma dan kadan ne. Idan kuma kana neman abinci mafi amfani ga jiki, to ai ba kamar wanda na tsiro ne, ba wanda aka jirkita shi a masana’anta ba.

Jikin dan Adam ya fi amfanuwa da saukin sajewa da abincin ainihi kan wanda aka jirkita yanayinsa, wato wanda aka sarrafa a tsarin masana’anta.

Ba gata ba ne ga lafiyar jikinka ka rika cin abincin masana’anta, irinsu indomi ko makaroni, kai hatta burodi wannan.

Baya ga karancin abu mai amfanarwa a cikinsu, suna kuma da illa a wani bangaren.

Wannan ya hada har da madara ta gwangwani ko ta leda a maimakon nono na asali, haka kuma dangin su lemon kwalba ko na roba, a maimakon ’ya’yan itatuwa.

Ka duba yanayinmu na mutanen yanzu da na baya, cututtukan zamani irinsu hawan jini da na sukari da su olsa duk sun ishe mu misali.

Haka sinadaran hada abinci irinsu sukari da magi da muke amfani da su, duk suna da illarsu, kamar shi magi musamman yana nakasa karfin namiji.

Kamar wadanne cututtuka ne kake samar da maganinsu?

Akwai magunguna da suka shafi na nau’ukan ciwon daji wato kansa da na ciwon zuciya da na ciwon koda da na kwakwalwa da na barin jiki da ya hada da farfadiya da danginsu, da na cututtukan ido da na karancin barci, da na hanta ciki har da irinsu hepatitis B, da na tsakuwar koda ko na mafitsara ko wata da ke zama cikin hanji, da na makoko da basur.

Wasu daga cikin cututtukan nan da na ambato yawanci magungunansu sai an yi fida a asibiti, wasu kuma ba a warkar da su sai dai a rika kulawa da su kawai a tsarin magunguna na zamani.

Amma a na tsirrai yawanci ana samun nasarar warkar da su dungurugum. Sannan magunguna ne da ba su da abin ki (todicity).

Wadanne nasarori ko ci gaba za ka ce wannan aiki ya samar maka?

Alhamdu lilLahi, sai godiya ga Allah da Ya huwace mini sanin magani da yadda za a yi amfani da shi. An samu waraka daga cututtuka masu sarkakiya ta dalilinsu.

Allah Shi ke kawo cuta kuma Shi ke warkarwa. Wasu daga cikin cututtukan an dauke su a matsayin wadanda ba a warkewa daga gare su amma cikin taimakon Allah sai ga shi an samu waraka.

Wannan aiki da nake yi ya fi mini duk wani aikin gwamnati na albashi da za a ba ni saboda ya ba ni abin da albashi ba zai bayar ba.

Kuma asirina a rufe ba wanda zai zo yau ya hura min wusir ya ce shekaruna sun kai 60 a duniya, ko na wuce shekara 35 ina aiki, dole sai a yi mini ritaya, ba ni da wannan fargabar.

Wane irin kalubale ke tattare da aikin naku?

Babban kalubalena bai wuce na sauran takwarorina masu magungunan tsirrai ba.

Gwamnati ba ta bai wa ayyukanmu muhimmanci. Ba ta yi da mu, ba ta taimaka wa ayyukanmu, sai na masu maganin zamani kawai.

Duk da cewa wani zubin su da kansu likitocin zamani, na turo majinyata wajenmu bayan sun ba da maganin sun yi allurar sun tsaga jikin, amma duk abu ya ki, kuma ana fara ba su na tsirran sai a samu nasara.

Tun a zamanin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Babangida, ya sa hannu a dokar amincewa da ayyukanmu, sannan ya hada mu da kungiyar likitoci ta Nigeriya wato MDCN, inda muke da kujera daya a kungiyar.

Sai dai inda matsalar take, duk kokari ko karatu da ka yi ba zai sa su ba ka lasisin aiki ba har sai ka yi nasu karatun.

Mun kai kuduri na kashin kanmu a Majalisar Dokoki ta Najeriya, inda muke neman a cire mu daga karkashinsu a ba mu gashin kanmu, amma a nan din ma sai su ka zaga suna yi mana zagon kasa.

Wannan ya hana mu zurfafa ayyukanmu kamar bude asibitoci na musamman kan wannan bangare da dai sauransu.

Kiranmu ga gwamnati ita ce ta duba ayyukanmu, ta duba rawar da takwrorinmu suke takawa a wasu kasashen duniya, ta ba mu gashin kanmu.

Wannan zai taimaka wajen tsaftace harkar da kawar da baragurbi da ke tsakaninmu. Rashin haka shi ya sa a yau kowa sai ya samu mota ya daura lasifika yana yawo kasuwanni da kauyuka a matsayin mai magani.

Wasu daga cikin ireiren wadannan mutane ba karamin cutar da al’umma suke yi ba wajen gurbata magungunan tsirrai.