Fitaccen lauyan nan mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Audu Bulama Bukarti, ya roki Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yafe wa matasan da suka yi masa bidiyon barkawanci har kotu ta hukunta su.
Lauyan ya yi kiran ne a cikin wani shirin bidiyo na kai tsaye da yake yi a shafinsa na Facebook tare da wasu ’yan jarida da kuma lauyan kare hakkin dan Adam a duk ranar Asabar.
- Zagin Ganduje a ‘comedy’ ya jawo musu hukuncin bulala 20 da share kotu na wata daya
- Mutum 2 sun gurfana a gaban kotu kan zargin bata sunan Ganduje a wasan barkwanci
A cikin shirin, Bukarti ya gayyato wanda ya yi bidiyon barkwancin, Mubarak Isa Muhammad, ya tattauna da shi tare da bin ba’asin yadda suka aikata laifin, da aka kai su kotu, da kuma yanke hukunci da aka yi musu kan laifin.
Bukarti shi da abokan gabatar da shirin, Abba Hikma Fagge da Ja’afar Ja’afar, da kuma Nasiru Zango, sun kalli yadda aka gudanar da shari’ar ta fuskar doka, inda suka bayyana abubuwan da suka kira kurakurai a yadda aka yi tuhumar, da tsare matasan, da kuma yanke hukuncin.
Amma, sun ce tun da wadanda ake tuhuma sun amsa laifi, har an yanke musu hukunci, babu abin yi illa su daukaka kara, ko kuma gwamna ya yi musu afuwa, la’akari da tasirin hukuncin zai yi a rayuwarsu nan gaba.
Ma’ana, dole nan gaba su bayyana cewa kotu ta taba hukunta su, wanda ke iya shafar wani matsayi, ko mukami na siyasa da za su nema.
A kwanan nan ne wani matashi Aminu Mohammed ya yi irin wannan tsokanar ga matar shugaban kasa a shafinsa na Twitter, inda ta sa aka gurfanar da shi gaban Kotu a Suleja.
Da kyar aka sako matashin bayan da uwargida Aisha Buhari ta janye karar da ta kuma yafe masa.