✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata Bahaushe ya tashi tsaye wajen kare martabarsa – Malami Doula

Bari mu fara da jin bayaninka, shin wane ne Malami? Sunana Abdulkadir Malami, ni mutumin Kamaru ne amma mahaifina mutumin Kano ne, nan cikin birni,…

Bari mu fara da jin bayaninka, shin wane ne Malami?

Sunana Abdulkadir Malami, ni mutumin Kamaru ne amma mahaifina mutumin Kano ne, nan cikin birni, a Kano aka haife shi, ni kuma an haife ni a Kamaru.

Idan mun fahimce ka, kai dai Bahaushen Kamaru ne, sannan kuma Hausawa na nan zaune a kasashen nahiyar Afrika har ma a wasu nahiyoyina duniya. To, yaya kake kallon yadda Hausawan can ke zaune a wuraren da aka ambata?

To, Bahaushe dai yana nan tun daga Kamaru, akwai a Ghana, akwai su a Gabon. Hausawa sun kasu kashi uku, farko akwai Bahaushe wanda yake shi yarensa ne. Na biyu kuma akwai Bafulatani ma yanzu bahaushe ne, Ba barbare ma yanzu Bahaushe ne. Na uku kuma akwai wasu kabilu da suka Musulunta, su ma sun zama Hausawa.

Idan aka tambaye ka cewa waye Bahaushe, me za ka ce?

A nan ni shi ne yanzu ni ma nake son in gane shin waye ne Bahaushe? Don mene ne ake zaginmu? Duk wani abu na mugun abu idan aka kawo sai a ce Bahaushe? Ba za a kawo abin kirki ba, duk wata lalacewa sai a kawo wa Bahaushe. Bahaushe da ake kawowa a farko a batun lalacewa, shi ke ba ni haushi. Ka ji ana cewa ai mu duk abin da ka yi da Bahaushe ya lalace.

Me kake tsammanin yake jawo wa Bahaushe zagi?

Abin da ya sa, kaunar mutane da yawa da yake yi da rashin kabilanci. Da Bahaushe yana da kabilanci kamar yadda sauran kabilu suke yi da ba a yi masa haka ba.

Ko ya kake ganin Hausawa mazauna kasar Kamaru ke rike al’adu da harshen Hausa?

Eh! Akwai al’adun da ba su canajawa, akwai al’adu da suke nan na aure na suna da haihuwa da sauransu. Al’adun duk iri daya ne, ba su canjawa amma akwai wadansu abubuwan da wada su ne suka akwo mana su, wadanda ba na Bahaushe ba ne.

Kamar wadanne a misali?

Kamar yanzu akwai wadansu al’adun da suke shigowa, za ka ga ka samu ko a yaren ka ga Bahaushe dai an san shi da kunya, an san shi da kara; Bahaushe kuma ya san nasa, duk inda Bahaushe yake idan ya ga dan uwansa in dai ya yi masa Haus, zai iya taimaka maka dan uwansa ne saboda haka ba zai bar ka ka tagayyara ba. To, akwai wasu da suka shiga suka boye cikin Hausa, yanzu akwai Bafulatani da zai nuna maka shi ba Bahaushe ba ne, ya tafi wani gari zai boye kansa, zai iya fitowa fili ya nuna maka shi ba Bahaushe ba ne ba, zai ce shi Bafulatani ne.

Me kake ganin ya haddasa suke yin haka?

Saboda Bahaushe shi yana son kowa da kowa.

Bari mu dauki wata al’ada daya da ake alakanta ta da Bahaushe, ita ce al’adar bara. Kana ganin cewa yin bara al’ada ce ta Bahaushe?

Bara ana alakanta ta da Bahaushe kuma Bahaushe ya rungume ta, ya yi mata muguwar fahimta kuma wa ya jawo masa? Malamai ne suka sanya bara ta zama wani abu, suka sanya ta a addini, wanda kuma addini bai yarda ba da kaskanci. A duk inda ka ga Bahaushe yau, a duk duniya babu wani mai yin bara sai Bahaushe, duk wata kabila a duniya ba mai yi sai Bahaushe. Idan na ce Bahaushe, duk wadannan kabilun fa sun shiga ciki, yau a duk inda ka tafi ko Kamaru ko Ghana ko Kwaddebuwa, in dai aka gan ka kana bara, sai a ce Bahaushe.

Bari mu taba bangaren shugabanci, ya dabi’ar Bahasuhe take a shugabanninsa?

Bahaushe a shugabanninsa yana son shugabaninsa to amma yana da saurin fahimta, yana da saurin rashin fahimta. Mene ne Bahasuhe, yanzun nan za ka ba shi labari, bai tantance ba sai ya yada. Yau abin kunya kamar yanzu a nan Najeriya, Bahaushen Arewa ya fito yana zagin Buhari Shugaban kasa; ba abin da ya fi wannan muni.

Ba ka gani ko hamayyar siyasa ce ta haddasa haka?

Siyasa da ta nuna kowa ya san halin da muke baya, kowa yanzu ya san halin da ake ciki. Yanzu mulkin baya idan za ka taso daga Kudu ka yo Arewa, a Kudu dariya ake yi maka, za ka taho gidan mutuwa. Yau an samu a Arewa ana kwanciyar hankali, ana zaman lafiya. Abin da Buhari Shugaban kasa ya danne wa ’yan Arewa wallahi sai bayan Buhari za a yi kuka, abin da ba mu fata, Allah Ya kiyaye. Don da muna ganin marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa muna zagi, bayan ya wuce Jonathan ya zo ai mun ga abin da ya haifar mana. Ai sarkin Kano ya yi wata magana a kwanakin ba ya.

Me sarkin na Kano ya ce?

Ya ce kowa ya ga abin da mulkin baya ya haifar mana, kada mu yi dariya. Masu fatar mutuwar Shugaban kasa, mutane su rika yin tunani kowa fa shi ma zai mutu, fatarmu Allah Ya ba shi lafiya; ya dawo ya ci gaba da yin mulkinsa amma wasu mutane ba su yin tunani me zai je ya dawo.

Mu kaddara wata daga cikin jami’o’in Nijeriya da ke Arewa ta shirya taro kan nazarin waye Bahaushe da kuma halayensa, ta gayyac ka bako mai jawabi, wace irin shawara za ka bayar a kasidar da za ka gabatar domin gyara hali?

Ni farkon abin da na ke so Bahaushe ya yi a nan, ya gyara shi ne mu hana bara. Barar nan a daina ta, a hana mutane tashi daga ko’ina zuwa kasashe yin bara. Sai ka ga mutum ya tashi daga nan Najeriya ko Kamaru, ya tafi bara kasar Kongo ko Koddebuwa, ba abin da ya tafi yi sai bara. Ya tafi idan ya samo kudin ba zai hana masa zama ya rufa wa kansa asiri ba. Kowa ya yaki bara, ba abu mai kyau ba ce. Farko, wallahi ranar da aka daina bara, ranar ce na san Bahaushe ya ci gaba. Yau idan ka tafi Kudu za ka ga sadaka-yallan nan da suke bara, ba Hausawa ba ne amma Hausawa ake kiran su. Mutanen Kudu duk wani dan Arewa Bahaushe ne, sai dai mu ne muke bambantawa amma dan Kudu babu ruwansa.

To, yanzu ina mafita?

Mafita ita ce ’ya’yanmu yanzu da suka taso suke da ilmi, su tashi tsaye su yaki wannan. Lokacin da Buhari ya yi mulkin soja mun yi asara, lokacin ne ya kamata a ce mun mora amma aka ture shi a mulki. A nan muka yi asara, da an bar shi da ya gyara kasar nan, da yanzu wadannan ’ya’yan da muka haifa da gyararru ne. Yanzu wadanda za a haifa nan gaba su ake son a gyara. Na yi farin ciki yanzu Bahaushe yana ci gaba a gaskiya. Da ba mu yin karatu amma yanzu kam mu Hausawa mun tashi tsaye da neman ilmin zamani. Shawarata a yi ilmi, ilmi shi ne babban ginshikin rayuwa.