✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a nemi ilimi kafin fara yabon Annabi – Sabuwar Fadar Bege

Mene ne tarihin rayuwarka a takaice? Sunana Aminu Abdullahi Hashim, an haife ni a karamar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano. Na fara karatun addini a…

Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?

Sunana Aminu Abdullahi Hashim, an haife ni a karamar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano. Na fara karatun addini a garin Gwarzo kuma har zuwa yanzu ina yi. A bangaren karatun boko kuwa na yi firamare da sakandare a Gwarzo. Sannan cikin hukuncin Allah na samu zuwa Kwalejin Ilimi ta Kumbotso inda na yi karatun NCE a bangaren zane-zane. A yanzu kuma ina gudanar da rayuwata a tsakanin Gwarzo da Suleja ta Jihar Neja, inda nake tare da dan uwana muna kasuwanci da neman ilimin addini.

Me ya ja ra’ayinka ka shiga wakar yabo?

Tun ina karami idan ina kallon fina-finan Hausa nakan yi sha’awar yin waka a wancan lokacin. Bayan na kammala  sakandare a shekarar 2005 sai na fara harkar wakokin Hausa, duk da cewa  babu wanda ya yi min jagoranci, amma na san ina sha’awar wakokin Zango don haka shi ne ya zame min madubi. A wancan lokaci nakan shigo Kano musamman saboda jarumi Zango, domin wani lokacin nakan je titin Gidan Zoo don kawai in gan shi duk da cewa ba na iya yi masa magana. Ina ganin ko tsoro ne ko kuma kunya ce ban san dalili ba. A haka dai sai na kama harkar wake-wake gadan-gadan. Kasancewar ina zama a Suleja kamar yadda na gaya miki  sai na yi wa Sarkin Suleja waka. Lokacin da na kai wakar gida sai ta yi wa mahaifiyata dadi inda ta ce min ina ma a ce Manzon Allah (SAW) na yi wa wakar da ta fi dadi. To ni kuma tun daga lokacin sai ya zama kamar ta ba ni wani haske shi ke nan na jingine duk wasu wakokin Hausa da nake yi na juya ga bangaren yabon Manzon Allah wanda har ya jawo mahaifiyata ta sa min sabon suna wato Sabuwar Fadar Bege, wato madadin marigayi Fadar Bege.

Zuwa yanzu wakoki nawa ka yi kuma ka yi kundin wakokinka?

Zan iya cewa na yi wakoki da dama sai dai har yanzu ban yi albam ba, duk da cewa mutane suna ta yin kiraye-kiraye a kan hakan. Amma abin da yake faruwa shi ne dole sai mutum yana da halin abu zai yi, ko a yanzu idan zan samu mai daukar nauyin albam din zan yi. Ba zan iya cewa ga yawan wakokina ba, sai dai duk a cikinsu na fi son wakar da na yi wa Nana Fatima ’yar Manzon Allah (SAW). Haka kuma batun albam na bar wa masoya Manzon Allah su buga.

Yawanci akan zargi sha’irai kan kalaman da suke amfani da su wajen yabon Annabi, wane mataki kake dauka a kan hakan?

Gaskiya ne, hakan na faruwa. Kullum yana da kyau mutum ya nemi ilimin abu kafin ya shige shi. Sai dai kuma kin san shi Manzon Allah mutum ne mai fadi kasancewarsa ba irin kowa ba, ya sanya wasu lokutan idan iliminka ya kai ka gaya masa wata maganar za ka fadi, sai dai kuma wanda kuma iliminsa bai kai ba sai ya ga kamar abin naka kuskure ne. Shi ya sa kullum nake fadi cewa dole ne tsakanin mu sha’iran da kuma masu saurarenmu sai mun nemi ilimi, domin zurfin karatun ne kadai zai iya fid da mu daga irin wannan zargin. A nemi ilimi shi ne mafita.

Ana zargin mawaka da rashin hadin kai, me ke jawo hakan?

Gaskiya a tsakanin masu yabon Annabi (SAW) za ki tarar wannan hassadar kadan ce ko ma zan iya cewa babu ita. Za ki ga duk inda muka hadu muna son junanmu tare da kaunar junanmu. Idan ma ana samun irin hakan to sai dai a sauran fagagen wakokin Hausa. Duk da cewa muna da bangarori na addini akwai fahimtar juna a tsakaninmu.

Wane sako kake da shi ga masoyanka?

Ina gaishe su tare da yi musu fatan alheri.