Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta bukaci Shugaba Buhari ya fadada haramcin da ya sa na shawagin jirage zuwa jihohin yankin da suke fama da matsalar tsaro.
Shugaban ACF, Cif Audu Ogbeh, ya ce akwai bukatar haramta shawagin jirage a jihohin Borno, Taraba da Binuwai inda ake zargin jiragen sama na kai wa ’yan bindiga da mayakan Boko Haram makamai a cikin dazuka.
An harbe mutum daya a Makarantar Jangebe
Mutum biyu sun mutu bayan karbar rigakafin Coronavirus
Shugaban na ACF ya yi kiran ne washegarin da Buhari ya ba umarnin hana zirga-zirgar jirage da kuma ayyukan hakar ma’adinai a Zamfara.
Mashawarci kan Tsaron Kasa, Babagana Monguno, ya sanar da matakin ne bayan an ceto dalibai mata 279 da ’yan bindiga suka sace a makarantar kwana ta GGSS Jangebe a Karamar Hukumar Talata-Mafara ta Jihar.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya shaida wa Aminiya cewa matakin yunkuri ne na dakile ayyukan masu taimaka wa ayyukan ’yan bindiga a Zamfara.
Garba Shehu ya ce an dauki matakin ne bayan zargin jiragen sama na wa ’yan bindiga fasakwaurin makamai zuwa cikin dazuka inda suke musayar makaman da zinarin da ake haka ba bisa ka’ida ba.
Tuni dai Gwamnan Jihar, Bello Muhammad Matawalle ya soki matakin, wanda yake cewa bai san hikimar da ke cikinsa ba.