✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a gayyaci Lukman Zakari a ’yan kwallon Eagles na gida – danjuma Manaja

Fitaccen manajan nan na ‘yan wasan kwallon kafa da ke Kaduna danjuma Hussaini wanda aka fi sani da Manaja ya yi kira ga mai horar…

Fitaccen manajan nan na ‘yan wasan kwallon kafa da ke Kaduna danjuma Hussaini wanda aka fi sani da Manaja ya yi kira ga mai horar da ‘yan wasan kwallon kafa na Super Eagles wadanda ke buga kwallo a cikin gida (Home Eagles) da ya gayyaci mai tsaron bayan nan Lukman Zakari wanda ya buga wa Najeriya wasannin a kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekaru 17 wato Golden Eaglets da na ‘yan kasa da shekaru 20 wato Flying Eagles.

danjuma Manaja wanda ake wa lakabi da babban Manaja ya yi wannan kira a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a gidansa da ke Unguwar Hayin Banki Kaduna, inda ya nuna cewa Lukman Zakari na da kwazo da aminci.

“Lukman Zakari amintaccen dan wasa ne, wanda ya san ya kamata. Na yi mamaki matuka da na ga ba a gayyace shi gasar cin kofin CHAN ba, duk da cewa yana nan.

“Wannan ne ya sa nake kira ga Koci Salisu Yusuf ya gayyace shi domin zai yi amfani matuka don yana kwarewar da ake bukata,” inji danjuma Manaja.

Sannan danjuma Manaja ya taya ‘yan wasan da ya yi sanadiyar tafiyar su Turai murnar yadda suke samun daukaka.

“Simon Moses yana kokari sosai a kungiyar KAA Gent, sannan kuma kwanan nan Inoocent Bonke ya koma Malmo FC, wanda wannan ba karamar nasara ba ce. Kuma ya kamata shi ma a gayyace shi kungiyar Super Eagles kamar yadda abokinsa Simon Moses ke ciki domin yana kwallo ne kamar Yaya Toure, kuma zai taimakawa Mikel Obi a tsakiyar fili..