✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a farfado da masana’antun da suka durkushe – Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya nemi gwamnatin Jihar Kano ta  farfado da masana’antun da suka durkushe ta hanyar zuba jari a…

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya nemi gwamnatin Jihar Kano ta  farfado da masana’antun da suka durkushe ta hanyar zuba jari a cikin masana’antun. Sarkin ya yi wannan kira ne a wajen taron koli na Kamfanin Zuba Jari na Jihar Kano (KSIP).

Sarkin wanda ya samu waklicin Hakilimn Tofa Dan Adalan Kano Alhaji Isyaku Umar Tofa ya ce ba wai matsalar rashin kudi ne ke  dakile kasar nan daga ci gaba ba, sai dai kawai ba a bude kofofin damarmaki ga jama’ar da za su kawo wani ci gaba da ya kamata.

“Kudi suna nan a zube abin da ya rage shi ne mutane su samu damar da za su yi aikin da za su gyara Najeriya. Don haka ya kamata a samar da wuraren ayyukan yi ga jama’a musamman a Arewa yadda kowa zai bayar da gudunmawarsa wajen karkade talauci daga yankin Arewa,” inji Sarkin.

A jawabin maraba Shugaban Kamfanin Zuba Jarin na Jihar Kano Dokta Jibrilla Mohammed ya ce sun shirya taron ne da niyyar lalubo hanyoyin da za a bi don warware  matsalolin da ke yi wa kamfanonin barazana.

“Kamar yadda kowa ya sani an kafa kamfanonin zuba jari a jihohin kasar nan da niyyar sama wa gwamnati kudaden shiga sai dai kuma saboda wasu dalilai mafi yawan kamfanonin ba su iya cimma manufar da aka kafa su a kai, hakan ya sa muka gayyato masu ruwa-da-tsaki don tattauna matsalolin tare da lalubo hanyoyin da za a shawo kansu  don a bunkasa arzikin jihohin da na yankin Arewa gaba daya,.” inji shi.

Da yake jawabin babban bako a wajen taron Shugaban Kamfanin (NNDC) ya bayyana takaicinsa game da yadda aka rasa banki ko da guda daya na Arewa, inda ya ce Kamfanin na NNDC yana iyakar kokarinsa wajen ganin ya janyo hankalin ‘yan Arewa don ganin sun sake samar da banki

mallakar Arewa da zai tsaya da kafafunsa. “Yanzu duk wani abu da muke yi da ya shafi kudi a Arewa ba mu amfana da shi, wasu ne can ke samun kudi  da mu. Mu mun zama sai dai mu raya wasu mu kashe kanmu. Ya zama dole mu yi harka da bankunan kasuwanci ,  Don haka kullum ina fadin cewa dole ne Arewa ta samu bankin kanta wanda hakan zai kara bunkasa tattalin arzikin yankin.”