✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kamata a farfado da kyakkyawar dangantakar Arewa da Kudu maso Kudu – Shugaban Matasan Ijaw

A kwanakin baya ne Shugaban kungiyar Matasan kabilar Ijaw, kabilar da Shugaba Jonathan ya fito, Mista Udengs Eradiri ya gana da manema labarai inda wanke…

A kwanakin baya ne Shugaban kungiyar Matasan kabilar Ijaw, kabilar da Shugaba Jonathan ya fito, Mista Udengs Eradiri ya gana da manema labarai inda wanke mummunar fahimtar da ake yi wa matasan Neja-Delta. Kuma ya bayyana cewa akwai kyakkyawar dangantakar siyasa a tsakanin yankin Kudu maso Kudu da ake kira Neja-Delta da kuma Arewa, inda ya bukaci a farfado da wannan dangantaka domi ci gaban kasar nan:

Za mu so mu san ka gabatar mana da kanka?
Sunana Udengs Eradiri, Shugaban Majalisar Matasan Ijaw na Duniya, ita wannan kungiya ita ce ta hudu a kungiyoyin kabilu a fadin Najeriya, kuma ita ce gaba wajen gwagwarmayar neman ’yanci ga mutanen yankin Neja-Delta a Najeriya. kungiyar Ijaw Youth Council IYC, tana da wakilai da suka fito daga jihohi Akwa Ibom da Ribas a Gabas. Yankin tsakiya da ya hada da Jihar Bayelsa; Yamma akwai jihohin Delta da Edo da Ondo. Kuma muna da rassan kungiyar a Legas da Abuja da kasashen Amurka da Ingila da Afirka ta Kudu. Manufar kungiyar, ita ce kare ’yanci da martabar mutanen Ijaw a duk inda suke a duniya. An kafa kungiyar IYC ce a 1998 bayan yekuwar Kayama, lokacin da kungiyoyin kare muradun yankin Neja-Delta suka hadu domin fuskantar rashin adalci da ake yi wa yankin da kuma mulkin danniya na gwamnatin soja a wancan lokaci. A lokacin mun amince da kafa kungiya babba guda daya domin tunkarar matsalolinmu. Haka kowane bangare ya amince muka samar da kuniya daya mai suna Ijaw Youth Council. Wannan ita ce kungiyar da ke gaba-gaba wajen gwagwarmayar samar wa kabilar Ijaw ’yanci a wadannan shekaru.
Ga duk dan Arewa da ya ji sunan Ijaw ko Neja-Delta, abin da zai zo zuciyarsa shi ne, sace-sacen jama’a da fasa bututun man fetur da sauransu. Me za ka ce dangane da haka?
To, na yi muku maganar rashin adalci tun daga farko. Na kuma gaya muku cewa IYC, kungiya ce da ta kunshi kungiyoyi daban-daban, wadanda kafin wannan haduwa suna da hanyoyin cimma muradunsu, har da na daukar makamai a wasu lokuta. Amma ita IYC ba ta tashin hankali ba ce, ba kuma ta daukar makamai ba. Ganin yadda wadancan kungiyoyi suke a da, yanzu kuma an hade su karkashin IYC, sai wasu ke kallon kungiyar ba ta zaman lafiya ba ce. Kasancewar shugabannin wasu kungiyoyin kwatar ’yanci a Neja-Delta, kamar su Tompolo da Itakpe da Asar-Dokubo da sauransu, ya ba kungiyar IYC wata fassara ta daban. Lallai IYC ba kungiyar tashin hankali ba ce, kuma mambobin kungiyoyin da ke cikinta a yanzu, wadanda a da suka yi abin da suka yi, halattatun ’ya’yan IYC ne. Ba don abin da suka yi a wancan lokaci ba, da ma ba ka ji sunan Neja-Delta ba, da kuma ba ka ji sunan IYC ba. Yunkurinsu ya taimaka wajen isar da sako. Dangane da maganar satar man fetur, wannan ya danganta da me ke faruwa ne. Gwamnatin Najeriya na samun arzikin man fetur, ba tare da la’akari da halin kunci da take jefa mutanen yankin da ake hako man fetur din ba. Gaskiya, mu mutane ne masu matukar hakuri da kawar da kai, amma da tura ta kai bango dole muka mike don neman hakkinmu. Wannan yunkuri ne ake kambama shi fiye da yadda lamarin ya ke, lallai ana satar man fetur, kuma magana a kan wannan lamari, yana da tsawon gaske. Amma ku sani, satar man fetur na manyan masu hannun da shuni ne. Mutanenmu talakawa ne, ba su da manyan jiragen da za su zo, su saci danyen man fetur, su yi waje da shi. Sai ka ga wasu a gwamnati da ’yan siyasa, za ka iya kawo mutane daga waje su zo su kwashi mai su fita da shi. Daga karshe dai man na komawa matatar man fetur ne, inda ake sayar da shi. Saboda haka satar man fetur ba wanda ake gani da ake sayarwa a kan tituna ba ne, magana ce babba da za a kwana ana tattaunawa a kai, kamar yadda na gaya muku.
Abin da zan ce a takaice shi ne, ba za ka iya satar man fetur a kasar nan ba sai ka zama hamshakin dan siyasa ko mai hannu da shuni. Talakawan da ka ga an sa su a lamarin, suna yi ne don samun abin da za su ci, amma manyan na boye. Abin da muke cewa shi ne, gwamnati ta tallafa wa jama’ar yankin da take hako man fetur a wurinsu, don sai mutum ya koshi zai yi rayuwa mai tsabta da ba zai fada cikin wannan mummunan aiki ba.
Ganin cewa yanzu harkar siyasa ta fara zafi a Najeriya, mene ne matsayin IYC a fagen siyasa?
A matsayinmu na IYC, muna alfaharin cewa a karon farko, mun samar da Shugaban kasa a Najeriya daga yankin tsiraru na Kudu, wanda ba a taba samu ba. Shugaba Goodluck Jonathan dan kabilar Ijaw ne. Idan ka duba tarihin Goodluck Jonathan, ba wai rana tsaka ya ga kansa a ofishin Shugabana kasa ba, gwagwarmayarmu a yankin Neja-Delta ta sa a kasar nan aka ga dacewar a samo wani daga yankin. Haka kuma ta kasance da taimakon Allah sai ga shi yankin Ijaw ya fitar da Goodluck Jonathan a matsayin Shugaban Najeriya.
A lokacin da aka nemi wani daga yankin Neja-Delta da zai zama Mataimakin Shugaban kasa ga marigayi Umaru‘Yar’aduwa, sai aka je bangaren Kudu maso Kudu aka zabo ban kabilar Ijaw. Ka san kuma yadda siyasa take, dole ka nemo wanda ya goge a kan abin da ake bukata. Gaskiyar lamari shi ne, gwagwarmayar IYC ta sa ’yan siyasa suka yi amfani da hankali wajen mayar wajen nemo wani daga kabilar Ijaw. Haka kuma aka yi, aka ciro Goodluck Jonathan cikin gwamnonin yankin, ba don ya fi su ba, sai kawai domin tasirin gwagwarmayar IYC da aka dade ana yi cikin kwarewa. Mu kamar Yesu muke, wanda ya zubar da jininsa don wasu su ji da dadi su rayu. Shi ya sa muka kasance a yankin Neja-Delta. A kan haka Jonathan ya zama Shugaban Najeriya, don haka ma yanzu nake zaune tare da ku a nan. Ba wai don shi a kashin kansa ba da kujerar Shugabancin kasar nan, ba wai domin shi a kashin kansa ba, sai don martabar kujerar, siyasa da tattalin arzikin kasa. Don haka, mu muka samar da kujerar shugabancin kasar nan. Shi ya sa idan kuka lura a maganganunmu da bayanai da muke fitarwa, za ku ga duk inda Shugaban kasa ya yi ba daidai ba, mukan jawo hankalinsa, mu nuna masa abin da ya kamata ya yi. Kun ga ke nan, ba wai muna nuna ikon cewa kujerar tamu ce mu kadai ba, muna nuna abin da ya kamata a yi ne don amfanin duk ’yan kasa, a matsayinmu na tsirarru da suka samar da shugabancin wannan kasa, domin a samu sahihi kuma ingantaccen shugabanci da zai amfani kowa.
Akwai wasu abubuwa a dunkule da suka shafi zaben 2015, muna da ra’ayin cewa ya kamata a ba Shugaba Jonathan wata dama ya ci gaba da mulki. A fannin noma, ya kawo ci gaba, haka idan aka duba a zamaninsa, a gina hanyoyi masu yawa a kasar nan, fiye da gwamnatocin da aka yi a baya, an gyara tashoshin jiragen sama, tare da samar da sababbin filayen jirage na kasa da kasa a kowane daga bangarorin kasar nan shida. A shekara hudu da wata 11 kacal, wannan gwamnati ta samar da sababbin jami’o’in tarayya fiye da 12. Akwai sabuwar jami’a ta koyar da tukin jirgin ruwa da gwamnatin ta samar da ba a taba samun irinta a tarihin kasar nan ba. Sakamakon yajin aikin malamai da aka yi fama da shi a lokutan baya, don kaucewa haka, sai Shugaban kasa ya samar da kudi a fannin ilimi. Yanzu jami’o’i na iya bayar da kwangiloli kamar yadda sauran ma’aikatu ke yi, don a samu ingantaccen ilimi. Haka Shugaban kasa ya sa makudan kudi a bangaren samar da wutar lantarki. Shi ya sa ake ta bude cibiyoyin samar da wutar lantarki ko’ina. Wutar lantarki ba karamin al’amari ba ne, sai a hankali, amma daga lokacin da wannan gwamnati ta shawo kan maganar hanyoyin raba wutar, matsalar rashin wuta a kasar nan za ta zama tarihi.
Yaushe rabonka da ganin jirgin kasa? Duk wani yaro dan kasa da shekara 28 bai taba ganin jirgin kasa ba a rayuwarsa. Amma yanzu ga jiragen kasa nan na zirga-zairga da safarar mutane da kayansu a fadin kasar nan, wanda hakan ya rage cinkoson ababen hawa a kan tituna da kuma hadurra. Yanzu haka tattalin arzikin Najeriya ya zamo na 26 a duniya, kuma na daya a Afirka, sakamakon mayar da hankali wajen amfani da kayan da aka sarrafa a gida. Yanzu kafin ka kawo kaya Najeriya, sai an tabbatar da cewa ba makamancinsa a cikin gida.
Sakamakon fadada fannonin da suka shafi man fetur, matasa yanzu sun samu abin yi da hakan ke tallafa wa rayuwarsu da bunkasa tattalin arzikin kasa. Shirin samar da mota kirar Najeriya ya sa kamfanonin kera motoci na kafa kamfanoninsu a kasar nan. Hakan zai bunkasa samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikinmu da kara kwarewar ’yan Najeriya a wannan fanni. A fannin sufurin jiragen ruwa, yanzu ba za shigo da jirgin ruwa ba, idan ba dan kasa a cikinsa a matsayin ma’aikaci ba, hakan ya kawo kwarewa ga jama’armu da shirya su wajen amfani da wannan kwarewa a cikin gida.
Laifin Shugaban kasa bai wuce irin makirice-makircen da kasashen waje ke shirya wa Najeriya ba. Cutar Ebola, an yi ta ne musamman domin Najeriya. Idan aka kalli yadda aka yi ta shigo kasar nan, tun daga filin jirgin saman kasar Liberiya ya nuna alamun kamuwa da cutar, amma duk da haka suka turo shi zuwa Najeriya. Sun yi haka ne don su samu kudi ta hanyar sayar da maganin cutar a kasar nan, su kuma nemi ba mu tallafi. Duk da haka, Najeriya ta shawo kan al’amarin ta mika musu kayansu can. Wannan shi ne babban laifin da Shugaban kasa ya yi. Haka kuma, ya ki amincewa da auren jinsi a kasar nan, kasashen Turai ba su ji dadin haka ba. Yanzu Najeriya na fitar da shinkafa don sayarwa a waje, kuma ita ce kasar da ta fi kowace samar da rogo. Hakan na nuna cewa tattalin arzikinmu na habaka. Wannan laifi ne, domin kasashen Yamma na jin haushin Najeriya ta dogara da kanta a fannin abinci, domin hakan barazana ce ga tattalin arzikinsu. Haka maganar take a fannin amfani da kayan gida, yanzu kamfanonin mai irin su Shell, an sayar da kaddarorinsu, don ba su da wani aiki da za su bayar, saboda tattalin arzikinmu na habaka. Yanzu Najeriya na aika injinyoyinta a fanni man fetur zuwa kasashen Ghana da sauran makwabta. Wadannan su ne wasu daga cikin nasarorin da Shugaban kasa ya samu; su ne kuma laifinsa ga kasashen ketare da hakan ya zame musu barazana. Sun fi so Najeriya ta jingina da su don su yi amfani da hukumomin rance, irin su IMF wajen danne mu, amma sai bunkasa take yi, Afirka sai habaka take yi. Shi ya sa ake ganin makirce-makirce iri-iri da suke bullo da su.
Saboda haka, ya kamata ’yan Najeriya su fahimci cewa Shugaban kasa yana da kyakkyawar manufa ga wannan kasa. Dubi makarantun almajirai da ya kafa a Arewa, nan da shekara goma ilimi a Arewa zai habaka matuka. Dalilin haka, ba za a samu wanda za a yi amfani da shi wajen miyagun ayyuka ba. Wadannan su ne damuwar da ’yan siyasa ke nunawa, don haka muna amfani da wannan dama wajen kiran jama’a su mara wa Shugaban Jonathan baya a zabe mai zuwa, don hakan zai amfani Arewa. Koyasuhe Arewa da Kudu maso Kudu suna tafiya tare a fannin siyasa, muna kallonsu a matsayin ’yan uwa. Shi ya sa muke rokonsu (’yan Arewa) yanzu, ku ci gaba da kasancewa ’yan uwan da muka sani a da, musamman a neman tsayar da Shugaban kasa karo na biyu. Idan kuka mara masa baya a karo na biyu, babu shakka za mu mara maku baya a 2019, lokacin da zai bar mulki. A lokacin duk wasu jam’iyyu, za su fitar da dan Arewa ne a dan takarar Shugaban kasa, dama siyasar a koyasushe tsakanin Kudu da Arewa take kasancewa. Ka ga ke nan, ya rage wa Arewa ta zabi dan takarar da ya fi cancanta. Mun san akwai ’yan takara nagari a Arewa, irin su Kwankwaso da El-Rufa’i da Atiku da sauransu. Wadannan mutane ne da suka yi aiki a matsayin da suka taka a baya, kuma an gani. Don haka muna rokon ’yan Arewa su mara mana baya a yanzu, don gobe mu mara wa ’yan siyasarsu masu tasowa su amshi ragamar mulki a 2019 don ci gaban wannan kasa.
Ko kana da wani sako ga jama’ar Najeriya?
Sakonmu ga ’yan Arewa ne, su mara wa Shugaban Jonathan baya don ya kammala ayyukan da ya faro, domin mu ma mu mara masu baya su yi shugabanci a shekarar 2019. Halin da wannan kasa ke ciki a yanzu yana da tsoratarwa. Muna da ra’ayin kasar nan ta zauna a dunkule, ana haifar da yanayin tsoratarwa a wannan zabe, don haka muna son haduwa da ’yan uwanmu matasa na Arewa don kawar da wannan yanayi. Mu samar da yanayin fadakar da jama’a don kauce wa tashin hankali a lokacin zabe, don matasa talakawa ne za a yi amfani da su. Dole mutum daya ne zai ci wannan zabe, don haka ba abin a mutu ko a yi rai ba ne. Muna fatan a yi zabe cikin kwanciyar hankali.