Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ce akwai bukatar a fara hukunta ’yan siyasar da ke amfani da addini a wajen yakin neman zabe.
Ya bayyana haka ne ranar Talata a Kaduna, yayin bikin bude ofishin Gidauniyar Bunkasa Zaman Lafiya da Ci Gaba ta Sarkin Musulmi.
- DAGA LARABA: Yadda Son Mata Da Dukiya Ke Raba Zumunci
- Muhimman abubuwan da suka faru a duniyar nishadi ta Najeriya a 2022
El-Rufa’i ya bayyana damuwarsa matuka kan yadda ya ce wasu ’yan siyasa na amfani da addini da kabilanci wajen raba kawunan al’umma a yayin kamfen dinsu.
Sai dai ya ce babban zaben 2023 zai ba ’yan Najeriya cikakkiyar damar kawo karshen masu ci da addini.
Gwamnan ya kuma yi kira ga Sarakuna da malamai da su yi addu’ar samun Shugaba na gari da zai hada kan kasa kuma ya ciyar da ita gaba a zaben da ke tafe a watan Fabrairu mai zuwa.
El-Rufa’i ya kuma nemi afuwar mutanen ya ce akwai yiwuwar ya bata musu a mulkinsa.
“Muna iya bakin kokarinmu wajen ganin mun yi komai daidai, amma Allah ne kawai ba ya kuskure. Saura na wata biyar na sauka, saboda haka nake neman afuwar duk wanda na saba wa. So nake na rika barci salim-alim bayan na sauka,” inji El-Rufa’i.
Shi kuwa da yake nasa jawabin, Uban gidauniyar, kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce gidauniyar ta sha tattaunawa da masu ruwa da tsaka daban-daban don ganin yadda za ta inganta rayuwar al’umma.
Shi ma Babban Jami’in gidauniyar kuma Sarkin Argugu da ke Jihar Kebbi, Alhaji Sama’ila Muhammad Mere, ya yaba wa Gwamnan Kaduna kan ba da kyautar fili da gudunmawar Naira miliyan 25 domin gina hedkwatar gidauniyar.