✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya gano sulallan Naira miliyan 10 da aka binne a gonarsu ta gado

Ana harsashen kudaden sun kusa shekara 80 a binne a cikin gonar

  • Iyayenmu suna da labarin kudin
  • Sama da shekara 80 ke nan da binne kudin
  • Za mu yi gwanjon sulullan ga gidajen tarihi

Wani mutum a garin Badejo da ke Karamar Hukumar Potiskum a Jihar Yobe ya gano sulallan da aka kimanta a kan Naira miliyan 10 a gonarsu ta gado da aka kiyasta sun shafe sama da shekara 75 a binne cikin wata tukunya.

Hakan ya sa al’ummar garin a farin ciki
saboda gano wannan abin tarihi.

Jaridar The SUN wadda ta ruwaito labarin ta ce mutumin mai suna Ibrahim Badejo da abokan aikinsa ne suka gano
wadannan sulalla da darajarsu ta kai Naira miliyan 10 a yanzu.

Ibrahim Badejo yana daya daga cikin jikokin mai gonar kuma wanda ya kafa kauyen mai suna Mai Shuwa Badejo.

Ibrahim Badejo shi ne Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwar Kamfanin Gonar Kakasku Blan Integrated Farm
and Hatchery da ke kauyen na Badejo.

Kafin hakan malamin na fafutukar neman kudin da zai je karo karatun digiri na biyu ne a fannin Biochemistry da Biology a Jami’ar Jiangnan, Wuxi, Jiangsu a China lokacin da cutar
COVID-19 ta bulla a shekarar 2020.

Ibrahim Badejo yana Najeriya ne lokacin da cutar ta bulla, don haka ya ci gaba da zama a kasarsa yayin da aka sa dokar hana fita.

“Bayan na dawo daga China saboda COVID-19, babu aiki,” kamar yadda ya fada wa jaridar The Sun.

“Kiwon kaji shi ne aikin da na fi kwarewa don haka na tattauna da mahaifina cewa ina son bude gonar kiwon kaji don samar da abincin kiwon kaji da kwai da sauransu.”

Mahaifinsa ya amince da haka amma Badejo ya ce babbar matsalar fara sana’ar da yake mafarki ita ce samun kudin gudanar da ita.

Amma sai ya sha alwashin ba zai bari wannan cikas ta hana shi cika mafarkinsa ba don haka ya sayar da kayansa ya yi rajistar kasuwancinsa da
Hukumar Kula da Kamfanoni.

Ta haka ne Badejo ya fara da kafa Gonar Kakasku Blan Integrated Farm and Hatchery, kamfanin yana samar da kaji da abincin kaji da takin gargajiya da kwai da kayan lambu.

Ya bude asusun hada-hadar kasuwanci ya fara samo kudade a ciki da wajen Najeriya, inda ya nemi tallafin sama da Naira miliyan 20.

“Na samu asusun saka hannun jari na matasan Najeriya da na fara da su, tare da fatar cewa wani abu zai taso kuma zan samu kudi a nan gaba,” inji shi.

Mahaifin Badejo ya rija nuna goyon baya ga burin dan nasa.

“Ya ba ni filin da ya gada daga mahaifinsa. Shi ma mahaifinsa ya gada daga mahaifinsa,” inji shi.

Matashin dan kasuwar ya ce ya samu kudin ne tare da tallafin jarin matasa yadda ya fara aza harsashin sana’ar kiwon kaji.

A cewarsa abin takaici, bayan wata takwas an dakatar da aikin ginin saboda karancin kudi.

Ya kara da cewa, “A watan Afrilun bara na nemi tallafi daga Hukumar USAID. Ina da wani sabon taki da nake amfani da shi don tsarawa gonar mahaifina.

Gwamnatin Amurka tana neman sababbin abubuwa wadanda za su habaka samar da abinci da aikin yi saboda cutar COVID-19 ta zo da asarar ayyuka masu yawa.

“Yawancin mutane sun dogara da albashi ne kuma kulle ya hana su fita aiki. Yawancin mutane ba za su iya zuwa gona ba kuma COVID-19 ta zo da matsaloli da yawa, don haka USAID ta bude shiri a matsayin wani bangare na
shirin gwamnatin Amurka a nan gaba,” inji shi.

A cewarsa “Sai na fara gudanar da wani aiki na samar da takin zamani na gida kuma wanda ba ya da wata illa na muhalli kuma yana iya zama a gona har tsawon shekara biyar ko, shida.”

“Na dauki sama da wata biyu kafin in cika dukkan takardun kuma ina yin haka dare da rana. Gaba daya shirin ya kasance ga ’yan Najeriya kawai kuma kungiyoyi sama da 4,000 ne suka nema daga Najeriya alhali su USAID suna neman kungiyoyi 33 ne kawai.

“A lokacin gwiwata ta yi sanyi cewa ba zan iya samun wannan tallafi ba. Wadansu mutane sun sa na karaya. Mun yi aikace-aikacen a matakin farko, na
cancanta kuma an daidaita ni, na gaba ya kasance mai himma kuma na yi nasara.

“An fitar da jerin sunayen karshe kuma na yi nasara kuma mun fara a watan Satumba. Tallafin ya samar mana da injina na zamani don samar da abinci na zamani,” inji shi.

Kamfanin Badejo ya fara aiwatarwa da shimfidar zauren ginin kaji a watan Janairun bana.

Yana aikin gina gonar kiwon kaji tare da wadansu ma’aikatansa ne sai suka ci karo da wata tukunyar yumbu dauke da makudan kudaden da aka binne a kasa.

“Wadanda suke aikin tona rami don mu yi amfani da kejin batur su ne Sama’ila Baba da Magaret Ayuba da Maryamu

Jeremiah da Yusuf Jibril Batele. Da farko mun yi mamaki don a zatonmu laya ce. “Bayan an bude tukunyar, sai muka ga sulallan kudi da yawa,” inji shi.

Badejo ya ce babu wanda ya san takamaiman inda aka boye kuxin amma mahaifinsa ya ba shi labarin cewa sun samu labarin an boye kudin bayan

gano su.

“Mahaifina ya gaya mani cewa mahaifiyarsa ta gaya masa cewa mai filin, wanda shi ne kakana, ya boye kudi a cikin kasa a gonar, amma ba su san

ainihin wurin ba.

“Ban san wannan labarin ba sai bayan ganowa. An yi imanin cewa Mai Shuwa Badejo, wanda ya kafa kauyen Badejo ne ya binne tukunyar kudin. Mutum ne mai matukar tasiri kuma hamshakin attajiri mai shanu da yawa. A cewar labarin, bai ma san adadin shanun da yake da su ba. Ya kuma shiga harkar noman amfanin gona.”

A cewar Badejo, kakansa ya sha haduwa da kuntatawa a wancan lokaci a hannun sarakunan gargajiya.

“Fadawan Sarki sai su zo gidansa su ce, ‘Sarki yana son babbar saniya. Akwai wani lokaci da suka ga wani babban rago a gidansa, suka ce sarki yana so kuma za su washegari su dauka.

“A daren nan ya ba da umarnin a yanka ragon, a ajiye masa fatarsa. Iyalansa suka ci naman ragon. Washe gari

fadawan suka zo sai ya ce musu ragon ya mutu, ’ya’yansa sun cinye. A wancan zamani, babu addini don haka mutane suna cin matattun dabbobi.

“Yayin da aka ci gaba da tsananta masa, akwai lokacin da yake tunanin yin hijira zuwa Gombe saboda zalunci.

“Lokacin da Turawa suka zo, sun so su ba shi takarda don ya zama sarki aji na farko, amma sarakunan zamanin suka yi adawa da hakan. Mahaifina, wanda yanzu ya haura shekara 70, yaro ne karami a lokacin kuma bai san kakansa sosai ba. Babban yayansa ne ya san shi amma ya rasu.

 

“Sulallan kudade da aka gano su ne kudade ne irin na Birtaniya. An samar da su ne a Birtaniya kuma an rarraba su a kasashen yammacin Afirka na Gold Coast (Ghana) da Najeriya da sauransu.

Akwai daya daga cikinsu na wajejen 1930 da sauransu. Mahaifina ya gaya mani cewa watakila an binne kudin ne a 1936 lokacin yana karamin yaro ko ma ba a haife shi ba. Mahaifina ya gaya mani cewa mahaifinsa yana da kudi a binne a wani wuri amma babu wani a cikin ’ya’yansa da ya san wurin. Amma sun san cewa kudi ne da yawa da aka binne a karkashin kasa.

“Ba mahaifina kadai ba ne kuma ko da an raba kudin zai samu kashi kadan saboda kakansa yana da ’ya’ya da yawa. Mahaifina shi ne da na biyu na karshe. Kakana ya kasance mai arziki amma mahaifina talaka ne.

“Ya rasu talaka amma ya sa mu a makaranta ya tarbiyyantar da ’ya’yansa wadanda suka zama manyan mutane a cikin al’umma a yau. Mahaifina ya ji takaicin abin da kakanmu ya yi saboda kudin zai iya zama garken shanu.

Tabbas ya sayar da shanu da yawa a kan wannan kudi. Kowane da na iyali yana so ya samu kudin da zai ajiye don gaba.

“Muna so mu yi gwanjon tsabar kudin ga duk wani gidan tarihi mai sha’awa, mutane ko cibiyoyin tarihi a ciki da wajen Najeriya,” inji shi.