✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya dace shugabannin ibo su taka wa mutanensu birki’

Shugaban kungiyar Izala reshen Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Inuwa dan Asabe ya bukaci shugabannin al’ummar Ibo na yankin Kudancin kasar nan da su taka wa…

Shugaban kungiyar Izala reshen Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Inuwa dan Asabe ya bukaci shugabannin al’ummar Ibo na yankin Kudancin kasar nan da su taka wa wasu daga cikin ‘yan uwansu birki da ke neman muzgunawa Hausawa da Fulani da ke zaune a yankin.
Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da dama ga duk dan Najeriya ya zauna a inda yake so, ba tare da wata tsangwa ba. saboda haka babu wani dalili da zai sa ace wasu kabila su bar wani yankin.
Daga nan ya ce, Najeriya kasa daya ce kuma wajibi ne mu yi hakuri da juna domin babu wata al’umma da za ta samu ci gaba da kwanciyar hankali, sai da zaman lafiya.
Har ila yau, ya ce babu addinin da ya kai Musulunci kaunar zaman lafiya kuma “duk inda ka samu Musulmi wanda yake da ilimi mutum ne mai son zaman lafiya domin Allah Ya tsine wa masu neman haddasa fitina a tsakanin al’umma,” kamar yadda ya bayyana.