✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace gwamnati ta tsawatar wa ‘yan kasuwa – Habibu Nalele

Mataimakin Shugaban  kungiyar ’Yan Kasuwa ta karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, Alhaji Habibu Lawal Nalele ya ce matukar ana son a magance…

Mataimakin Shugaban  kungiyar ’Yan Kasuwa ta karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, Alhaji Habibu Lawal Nalele ya ce matukar ana son a magance matsalar tsadar kayayyakin da ake fama da ita a kasar nan, wajibi ne gwamnati ta sanya idanu a kan kamfanonin da suke sarrafa kayayyaki da manyan ’yan kasuwar da suke fita zuwa kasashen waje su kawo kayayyakin.
Alhaji Habibu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, inda ya ce: “‘Yan kasuwa a kasar nan suna cikin wani mummunan hali, saboda duk wani tashin farashin kayayyaki da ke faruwa a kasar nan ana kuka da su ne. Ya zama dole a yi kuka da ’yan kasuwa, domin su ne suke gudanar da harkokin kasuwanci.”
Daga nan ya yi bayanin cewa   matsalar tashin farashin kayayyaki a kasar nan, akwai laifin gwamnati akwai kuma laifin wadansu ’yan kasuwa. Ya ce laifin gwamnati kan wannan matsala shi ne ta ki daukar matakai kan ’yan kasuwa da kamfanoni. Ya ce  manyan ’yan kasuwa da suke fita waje su kawo kayayyaki da kamfanonin da suke sarrafa kayayyaki su ne suke kara farashin kayayyakin a kullum.
“Yanzu harkokin kasuwanci  sun zama kamar jari-hujja a kasar nan, kowa yana abin da ya ga dama ne. Ya kamata gwamnati ta dauki matakai ta sanya dokoki kan manyan ’yan kasuwa da suke fita waje da kamfanonin da suke sarrafa kayayyaki a kasar nan da kananan ’yan kasuwa kan yadda za su rika sayar da kayayyakinsu,” inji shi.
Ya ce babu shakka wannan zai taimaka wajen magance matsalar tashin farashin kayayyakin a kasar nan.
Har ila yau, ya ce amma idan gwamnati ba ta tsawatar wa kamfanoni da ’yan kasuwa ba, ta ci gaba da barin kowa ya je ya ci gaba da yin abin da ya ga dama, to za a ci gaba da samun matsalar tashin farashin kayayyaki a kasar nan.