Wakilan Aminiya sun zagaya don jin ra’ayoyin mutane game da yadda ake shirin janye sojoji a yankunan da ake rikici a sassan Najeriya, inda suka bayyana ra’ayoyinsu a kan wannan shiri kamar haka:
Ba na goyon bayan janye sojoji – Muhammad Alabira Nabordo
Daga Umar Akilu Majeri Dutse
Ba na goyon bayan a janye sojoji daga yankunan da suke fama da rikici musamman yankunan da suke fama da rikicin Boko Haram.
A ganina lokaci bai yi ba da za ace gwamnatin za ta janye sojoji daga yankunan da suke fama da rikici, saboda idan aka janye su an bai wa barayi damar satar mutane su kuma barayin shanu su samu damar satar shanun jama’a yayin da su kuma ’yan Boko Haram za su samu damar shiga kauyuka suna kashe jama’a suna kwashe dukiyarsu. Kuma maganar da wadansu ke yi cewa akwai zargin da ake yi wa sojoji na cin hanci, don an kai su bakin daga hakan karya ne, idan sun yi akwai sauran jami’an tsaron da ba su kishin kasa su ma suna yi.
Ina goyon bayan janyewar –Alhaji Shu’aibu Zannuwa
Daga Jon D. Wada, Lafiya
Kantoman Yankin Raya Kasa na Lafiya ta Gabas a Jihar Nasarawa. Ina goyon bayan matakin janye sojoji a wadannan yankuna da ake rikici. Dalili kuwa shi ne, dama wannan ba aiki ne da ya rataya a wuyan sojoji ba. Ya kamata ’yan sanda ne su gudanar da aikin. Amma saboda wasu matsaloli musamman na rashin isassun kayayyakin aiki da inganta jin dadin ’yan sandan da sauransu suka sa ake tura sojoji. Saboda haka ya kamata a janye su, amma kafin a yi haka ina shawartar gwamnati ta bari su yi aiki da ’yan sanda na wani lokaci don su samu kwarewa a aikin kafin daga baya a bar su su ci gaba.
A janye sojojin a bar ‘yan sanda – Alhaji Ibrahim Hussaini
Daga Umar Akilu Majeri Dutse
Ya dace a janye sojoji a yankunan da ake fama da rikici a Najeriya a bar ’yan sanda su yi aiki. Saboda ai dama tun asali rikicin ne ya yi muni shi ya sa aka kawo sojoji, don magance rikicin. Yanzu tunda sojoji sun yi nasara a kan yaki da wadanda suke hana zaman lafiya a Najeriya, sai a bar ’yan sanda su ci gaba da tsaro da kare lafiyar al’umma da dukiyar talakawa. Gwamnati ta gwada yin hakan idan an samu nasara shi ke nan, amma al’amarin haka ba tare da an sanya ’yan sanda ba, za su rike ita kanta gwamnati, ba za ta fahinci yadda abubuwa da suke tafiya ba saboda watakila akwai wani daurin boye da ake mata, idan ta yi haka za ta iya fahimtar idan akwai wata matsala ta gyara.
Ina goyon bayan janye sojojin – Alhaji Husseini Abdullahi
Daga John D. Wada, Lafiya
Shugaban Kungiyar ’Yan lemo na Maraba a Jihar Nasarawa. A gaskiya a yanzu idan aka gudanar da bincike a yawancin wadannan yankuna da ake rikici a kasar nan za a gano cewa, al’ummomin yankunan suna korafi cewa sojojin da aka tura don kare lafiyarsu da dukiyarsu suna cutar da su ne maimakon ba su kariya. Sojojin kan kwace musu dukiya da suka hada da abinci da cin mutuncinsu da kwace musu tallafin da suke samu daga waje da sauransu. Saboda haka idan za a janye sojojin a kuma bullo da sabon salon tabbatar da tsaro a yankunan kamar yadda Gwamnan Jihar Borno ke yi a yanzu ba shakka hakan zai dace matuka.
Ban goyi bayan a janye sojoji ba – Ibrahim J. Mahmud
Daga Adam Umar, Abuja
A gaskiya ban goyi bayan a janye sojoji daga wadancan yankuna ba. ’Yan sanda da ake cewa za a maye gurbin sojojin da su ba na jin za su iya wadatarwa, saboda matsalar rauni da kuma cin hanci da ta fi muni a bangarensu. Ya kamata gwamnati ta kara karfafa sojojin da kayan aiki da kuma karin walwala.
Ko kadan ba na goyon baya– Jamilu Sa’idu
Daga Adam Umar, Abuja
Saboda duk da kasancewar sojoji a wasu daga cikin wuraren har yanzu akwai matsalar tsaro. Misali jihata ta Zamfara da ake cewa, an samu zaman lafiya kusan abin a rediyo da jarida ne kawai. Yankuna da ke kudancin Gusau da Dan-Sadau da kuma Maradun duk da cewa kashe-kashen ya ragu, har yanzu ana kai hari kuma idan an janye su harin yana iya kara ta’azzara.
Ina goyon bayan janye sojojin – Alhaji Husseini Abdullahi
Daga John D. Wada, Lafiya
Shugaban Kungiyar ’Yan lemo na Maraba a Jihar Nasarawa. A gaskiya a yanzu idan aka gudanar da bincike a yawancin wadannan yankuna da ake rikici a kasar nan za a gano cewa, al’ummomin yankunan suna korafi cewa sojojin da aka tura don kare lafiyarsu da dukiyarsu suna cutar da su ne maimakon ba su kariya. Sojojin kan kwace musu dukiya da suka hada da abinci da cin mutuncinsu da kwace musu tallafin da suke samu daga waje da sauransu. Saboda haka idan za a janye sojojin a kuma bullo da sabon salon tabbatar da tsaro a yankunan kamar yadda Gwamnan Jihar Borno ke yi a yanzu ba shakka hakan zai dace matuka.