A lokacin da nake aiki na samu zuwa kwasa-kwasai masu yawa, amma bari na zayyana maka kadan daga cikinsu: Na je wani kwas a kan Change Management a garin Jos da wata kungiya ta shirya, na je kwas kan harkokin sadarwa da tsare-tsare kan
sha’anin mulki wato Media Planning, Information and Secretary Work a shekarar 2001 da hukumar gidan talabijin na Bauchi suka shirya. Har ila yau, na je wani kwas
a Abuja wanda NIPR da Chartered institute of Public Relation UK
Information Conference suka shirya a shekarar 2010. Na je kwas kan yadda ake sarrafa waken suya a garin Bauchi a shekarar 1991 da dai sauransu.
Hakazalika, ni mamba ce kuma na rike mukamin Sakatariyar
kudi ta kungiyar NIPR Nigerian Institute of Public Relation, lokacin
muna Bauchi, na kuma zama Mataimakiyar shugaba ta wannan kungiyar da muka dawo Gombe. Har ila yau, na rike mukamin Jami’ar hulda da jama’a ta kungiyar ma’aikatan samar da hasken wutar lantarki reshen Gombe. Kuma na taba zama jami’ar hulda da jama’a ta kulub din kwallon gora na Bauchi, na zama shugabar kungiyar mata Musulmi ta kasa FOMWAN ta Jihar Gombe, na je kasashen kamar Saudiyya da Birtaniya da Italiya da Sweeden da Kanada da Faransa da kuma Indiya.
Kasancewa ta uwa, ina mai bai wa iyaye shawarar su sa ‘ya’yansu mata a makaranta don su sami ilimi duk da dai ni ban yi ilimi mai zurfi sosai ba, ina kiransu da su sa ‘ya’yansu domin ilimin mace abu ne mai kyau.
Wane dalili ya sa kika shiga siyasa?
Na shiga siyasa ne domin a fafata da ni a wasu bangarorin ganin cewa
akwai karanci mata a harkokin siyasa. Domin a nan yankin arewa idan mace ta shiga siyasa, ganinta ake kamar karuwa ce kuma rashin shigarmu ya sa a kan bar mu a baya sosai. Wannan kuma ya sa da kyar ake ba mu kashi 35 cikin 100 wanda muke nema a mukaman gwamnati.
Ko kina da wani buri a rayuwa?
Bani da burin da ya wuce na ga ‘ya’ya mata sun sami ilimin addini da na zamani saboda a dinga kwatance da su ganin cewa a nan arewa an bar mata sosai a baya bayan kuma su ne ke da hakkin tarbiya da gyaran gida, amma ba a ba su dama su ma ‘ya’ya ba ne.
Ya maganar iyali fa?
Ta fuskar iyali kuma ina da ‘ya’ya hudu, biyu maza, biyu mata.
Ya dace a ilmantar da ’ya’ya mata – Kwamared Maryam Isa 2
A lokacin da nake aiki na samu zuwa kwasa-kwasai masu yawa, amma bari na zayyana maka kadan daga cikinsu: Na je wani kwas a kan…