✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya dace a ilmantar da ’ya’ya mata – Kwamared Maryam Isa

Kwamared Maryam Isa Mele, tsohuwar jami’ar hulda da jama’a ta hukumar samar da hasken wutar lantarki ta kasa ce wato PHCN. Hakazalika, tsohuwar babbar mai…

Kwamared Maryam Isa Mele, tsohuwar jami’ar hulda da jama’a ta hukumar samar da hasken wutar lantarki ta kasa ce wato PHCN. Hakazalika, tsohuwar babbar mai bai wa Gwamnan Jihar Gombe  Ibrahim Hassan dankwambo  shawara ce a kan harkokin siyasa. Aminiya ta samu tattaunawa da ita don jin tarihinta da kuma irin kalubalen da ta fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance:

Za mu so ji takaitaccen tarihin ki?
Da farko sunana Kwamarade Maryam Isa Mele, ni Bateriya ce ’yar asalin JiharGombe, sai dai an hai feni ne a garin Kaduna kimanin shekaru 50 da suka wuce. Bayan an yayeni sai iyayena suka dawo garin Bauchi da aiki kuma a nan na girma har aka sani a makarantar firamare ta darikar Katolika, wadda daga baya aka mayar da ita St Peters, amma yanzu ta koma Wunti Primary. A tsakanin shekarun 1968 zuwa 1974 na yi aji bakwai daga nan sai na tafi Sakandaren ’yan mata ta garin Maiduguri wato GGSS a shekarar 1974 zuwa 1979. Ita ma yanzu an sauya mata suna ta koma Go bernment Girls College wato (GGC). Ina kamala wa sai na tafi BACAS Bauchi College of Art and Science a shekarar 1979 zuwa 1980. Na yi sharar fage bayan na gama maimakon na ci gaba na tafi jami’a, sai aka ce a’a. Daga nan  aka yi mini aure a shekarar 1980. A shekarar 1983 sai muka tafi kasar Amurka da maigidana da yake yana aikin jakadanci ne.
A shekarar 1987 sai muka dawo Najeriya, duk da cewa na samu dama a kasar Amurka, amma maigidana bai bar ni na yi karatu ba, kodayake, shi ya ci gaba da nasa har sai da ya samu digiri na uku. Har ila yau, ni ma  na yi aikin koyar wa na wucin gadi a makarantar renon yara wato Nurseryda ake kira Play Class. Bayan dawowarmu Najeriya sai aurena ya kare da maigidana. A nan ne na dawo garin Gombe a shekarar 1988 ina gida zaune sai na samu aikin koyarwa da karamar hukumar Gombe  Local Education Authority a matsayin malamar firamare, inda aka tura ni makarantar firamaren Bubayero a shekarar 1990, na fara aiki da shekara daya sai aka mayar da ni Firamarin Central da ke Gombe a shekarar 1991, ina koyarwa a shekarar 1992 sai na sake koma wa BACAS karo na biyu, inda na sake shiga ajin sharar fagen shiga jami’a wato IJMB. Da ana ci jarrabawa ta sai na tafi jami’ar Bayero ta Kano, na yi difloma a bangaren mulki da harkokin al’umma Public Administration.
Bayan na kammala sai na tafi Abuja neman aiki cikin ikon Allah sai na samu aiki da hukumar samar da hasken wutar lantarki ta kasa wato (NEPA) a watan Oktoban shekarar 1997. Lokacin da na cika shekara guda a Abuja ganin kuma yanayin rayuwar Abuja yadda take, sai na nemi sauyin wajen aiki aka dawo da ni ofishin gunduma a garin Bauchi a matsayin jami’a a bangaren mulki, a lokaci daya ina hadawa da aikin PRO wato jami’ar hulda da jama’a na hukumar idan jami’in hulda da jama’ar baya nan.
A shekarar 2006 ganin kwarewata a wannan fanni sai aka mayar da ni babbar jami’ar hulda da jama’a ta NEPA ta Bauchi gaba daya. Har ila yau, a watan Satumbar shekarar 2012 sai aka sauya mini wajen aiki aka dawo da ni Jihar Gombe a wannan matsayi nawa na jami’ar hulda da jama’a, amma a lokacin an sauya wa NEPA din suna ta dawo PHCN, a watan Nuwamba kuma 2013 sai na  yi ritaya na bar aiki. Ina ajiye aikin sai Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo na Jihar Gombe ya dauko ni ya ba ni mukamin siyasa, inda ya nada ni babbar mai taimaka masa kan harkokin siyasa wato SSA.
Wadanne kalubale kika fuskanta a rayuwaki?
A gaskiya kasancewa ta mace na fuskanci kalubale sosai a wannan aiki na hukumar samar da hasken wutar lantarki, saboda a duk lokacin da na fita kar bar kudin wuta a wajen kwastomomi za ka ga wasu na zagina suce mu ’yan iska ne.  Wasu su ce karuwa har gurde mini hannu wani ya ta ba yi, amma duk da wadannan  Allah Ya sa an kammala lafiya.
Ta fuskar nasarori fa?
Eh, na samu nasara sosai duk da cin mutunci da na dinga fuskanta na
wasu, amma babbar nasarar da na samu ita ce na koyi darasi na yadda zan zauna da kowanne irin mutum, kuma wannan aiki ya ba ni dama na shiga harkokin kungiyoyi sosai inda na kara sanin wasu matsalolin jama’a.