Wata Babbar Kotun Majistare da ke Zariya a Jihar Kaduna, ta ba da umarnin tsare wani matashin a gidan gyaran hali saboda yunkurin halaka mahaifinsa ta hanyar daba masa wuka yana Sallah a masallaci.
Ana tuhumar matashin ne mai kimanin shekara 21, wanda mahauci ne da yunkurin kisan kan mahaifin nasa, lokacin da yake Sallah a wani masallaci a unguwar Rimin Tsiwa a Zariya.
- Gudun sharholiya ne ya dawo da ni daga Amurka ranar ‘birthday’ dina – Buhari
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ke Jawo Asarar Rayuka A Kan Hanyoyin Najeriya
An gurfanar da matashin ne wanda ke zaune a Unguwar Karfe bisa zargin yunkurin aikata kisan kai.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Ramatu Dalhatu, wacce ta ki amincewa da bukatar matashin ta bayar da shi beli, ta ba da umarnin sakaya shi a kurkukun Zariya, har zuwa lokacin da Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna za ta bayar da shawara a kan lamarin.
Ta ce bisa tanade-tanaden sassa na 240 da 293 da 199 na kundin ACJL ma 2017, kotun ba ta da hurumin sauraron karar.
Daga nan ne ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 17 ga watan Janairun 2023.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Sarki Abdullahi, ya shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na ranar Laraba, 14 ga watan Disamban 2022.
Ya ce wani mai suna Muntari Musa ne ya cafke wanda ake zargin sannan ya mika shi ga ofishin ’yan sanda na birnin Zariya.
Ya kuma ce an sami nasarar kwace wuka da jini a jikinta daga hannun matashin.
ASP Sarki ya ce matashin ya yi amfani da wukar wajen caka wa mahaifin nasa sai biyu a baya, lokacin da yake Sallah.
Laifin, a cewar dan sandan ya saba da sassa na 240 da 293 da kuma 199 na Kundin Laifuka na Jihar Kaduna na shekarar 2017. (NAN)