✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar lantarki: TCN ta bude rassa a Katsina da Jalingo

Kamfanin wutar lantarki (TCN) ya kafa cibiyoyin gudanar da ayyuka biyu a Katsina da Jalingo a karkashin yankunan Kaduna da Bauchi. Kakakin TCN Misis Ndidi…

Kamfanin wutar lantarki (TCN) ya kafa cibiyoyin gudanar da ayyuka biyu a Katsina da Jalingo a karkashin yankunan Kaduna da Bauchi.

Kakakin TCN Misis Ndidi Mbah, ta ce an bude su ne domin raba ayyuka da kara wa wutar inganci da saukin gyara karkashin kamfanonin rarraba wutar na Kaduna da Yola.

Ta ce cibiyar da ke Katsina na da kananan tashoshi uku masu karfin wuta 200MVA a Katsina da Kankia da Daura da suke kan layin wuta mai karfin 132 kilovolts (KV).

An kuma gina wasu kananan tashoshi a karkashin cibiyar ta Katsina domin samar da karin 780MVA na wutar lantarki.

Ta ce Katsina da ke samun wutarta daga Kano a layuka biyu na 132kV, na bukatar a kara karamar tasha lantarki mai karfin 120MVA a Karamar Hukumar Mashi da har yanzu ba a fara ba.

Cibiyar gudanarwa ta Jalingo, na samun lantarkinta kan layi mai karfin 132kV daga babbar tashar Yola.

Jalingo na da kananan tashoshi hudu da ke dauke da 335MVA a Jalingo da Wukari da Takum da kuma Kashimbila.