✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wutar lantarki ta kashe mutum 2 a Jos

An tabbatar da mutuwar mutum biyu sanadiyyar tangardar wutar lantarki a mahadar Dadin Kowa da ke Jos ta Kudu a jihar Filato. Majiyarmu ta gano…

An tabbatar da mutuwar mutum biyu sanadiyyar tangardar wutar lantarki a mahadar Dadin Kowa da ke Jos ta Kudu a jihar Filato.

Majiyarmu ta gano cewa, wadanda suka rasun matasa ne masu aikin gini da ke ginin sabon bankin United Bank for Africa (UBA), da ake ginawa a unguwar Dadin Kowa lokacin da hadarin ya faru.

Hadarin wutar lantarkin ya rutsa da matasa uku  ne biyu daga ciki suka rasu dayan kuwa jinya a asibiti.