✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wurinmu Gwamnatin Tarayya ta koyi tsarin makarantun allo na zamani – Mai Tafsiri

Alhaji Musa Garba Mai Tafsiri shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Raya Addini kuma mukaddashin shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya ta Jihar Sakkwato, Aminiya ta zanta da shi…

Alhaji Musa Garba Mai Tafsiri shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Raya Addini kuma mukaddashin shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya ta Jihar Sakkwato, Aminiya ta zanta da shi kan abubuwan da suka shafi wuraren da yake jagoranci, tsawon lokacin da gwamnatin jihar ta dauka wajen kafa ma’aikatarsa da sauransu:

 

Alhaji Musa Garba Mai TafsiriAminiya: Wadanne irin ayyuka ne wannan ma’aikat taka ta aiwatar don ci gaban al’ummar Musulmin Jihar Sakkwato?
Mai Tafsiri: A gaskiya sai mu gode Allah an yi abubuwa da dama kamar wadanda suka fado ko aka yi tunaninsu ko za a nemi su a nan gaba. Wadanda muka gada su ne gina masallatai da makarantun Islamiyya da gyaransu, bayan wadannan mun yi abubuwan da suka tisgo wato fadada masallatai da sanya musu kayan zamani da suka dace da lokaci. Wadanda muka yi don gaba su ne gina makaratar allo ta zamani kuma an yi nasara a cikin wannan shirin domin ko
Gwamnatin Tarayya a wurinmu ta koya, kuma duk wata jiha da ke aiwatar da shirin sai a gaya mata ta zo Sakkwato ta koya ka ga an samunasara don kusan jiha takwas suka zo suka koyi shirin kuma za su gabatar da shi. Kwamitin Zakka da gwamnati ta kafa ma’aikatarmu mun samu ana ba shi Naira dubu 500 ne, amma yanzu Mai girma Gwamna ya sa jiha na ba shi Naira miliyan biyu, kowace karamar hukuma ta ba da Naira dubu 250 suka kama fiye da Naira miliyan 31, inda muke da kwamitoci goma da muke raba wa wadannan kudade. A kowane wata mukan ba kwamitin lafiya Naira miliyan shida da za a ki ba da kudin nan da ba ka san irin kukan da jama’a za su yi ba, don da su ne ake tallafa wa marasa karfi, ake kai su inda za su nemi lafiya ta jiki ko gyaran kashi a wata jiha ko kasa.
Aminiya: Wace rawa ma’aikatar ta taka wajen bunkasa ilimin addini da harshen Larabci?
Mai Tafsiri: Bayan kafa wannan ma’aikata mun dubi yadda martabar Sakkwato take, ba wani abu fiye da kula da addini. Ganin sha’anin Larabci ya yi kasa a jihar sai muka canja daukar nauyin karatun yara daga zuwa Bulgeriya ko Ingila muka maida zuwa Sudan da Masar da sauran kasashen Larabawa. Tunaninmu idan aka samu injiniya ko likita, to yana jin larabci.
Aminiya: Galibi mabarata sun fito ne daga Arewa, yaya lamarin yake a nan jihar?
Mai Tafsiri: Lokacin da aka koro mabarata daga Legas da namu suka dawo gida sai muka sa a dauki sunan duk wani mai bara a jihar nan don tallafa musu inda a kowane wata gwamnati ke kashe fiye da Naira miliyan 45 don tallafa musu. Tallafin ya sa wasu sun daina bara wasu kuwa sun ja jari ’yan kasuwa ne a yanzu.Wannan abu ya yi nasara sosai, an yi hadin gwiwa ne da Ma’aikatar Jin Dadin Jama’a. Game da ciyar da mutane abin buda baki a lokacin azumi gwamnati ta kashe fiye da Naira biliyan daya a shekarun da suka wuce. Kuma mukan tallafa wa marayu da kayan Sallah da naman Sallah kamar yadda duk wani mai uba ke samu. A bana mun kashe fiye da Naira miliyan 20. Mukan raba wadannan kaya ne a gundomin jiha baki daya.
Muna gyara wa masu karamin karfi gidajensu, misali akwai wata mace a daminar da ta wuce dakinta ya rushe ba ta da wanda zai gyara mata, mu ne muka yi dawainiyar yi mata gyaran. Kuma saboda kwazon Gwamnanmu ne ya sa aka kawo ofishin kungiyar Musulmi ta Duniya nan, a matsayin na shiyyar Afirka. Idan na ce zan ci gaba, zan dade ban kare zayyanowa ba, shi ya sa wannan ma’aikata ake kiranta komai da ruwanka, mun yarda da wannan suna don addini ba abin da ya bari.
Aminiya: Duk abin da aka ce akwai nasara to dole akwai kuma matsala, wadannan matsaloli ma’aikatarka ke fuskanta?
Mai Tafsiri: Matsalolin da muke fuskanta, ban dauke su wani abu ba, saboda mun riga mun janye kafar wandonmu domin yin maganinsu. Babba daga ciki shi ne rashin gaskiya. Za ka ga mutum ya zo mana da takardar karya ta magunguna masu tsada, in aka ba shi sai ya je wani dakin sayarda magani ya sayar. To amma yanzu mun gane, wani ya zo ya ce ya karye ko ba ya da lafiya to duk mun bar wannan ko da za mu yi laifi. Kwanan baya ma wata mace kudin aiki zuwa Kano ba su tafi ba, suka tafi Fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi don sake neman tallafi wurinsa can muka kama su. A yanzu masu musulunta ne kawai ake fama da wasu batagarinsu, shi ma dai ana samun nasara wurin kawar da matsalar.
Aminiya: Duk da kwamitocin da kuke da su da hukumar taimaka wa gajiyayyu ba su hana wasu yawon bara a jihar nan ba, ko akwai wani shiri da kuke yi na hana bara kamar yadda Jihar Kano ke shirin yi?
Mai Tafsiri: To shi wannan abu yana da wuya kwarai da gaske. Mun yi rajistar mabarata birni da kauye, wadanda ke bara a yanzu baki ne ba su cikin rajistarmu shi ya sa lokaci-lokaci Gwamna ke ba mu umarni cewa duk wanda aka samu yana bara a yi masa rajista a ci gaba da tafiya, wannan ke nan. Na biyu akwai masu taurin kai duk almajirin da ke tafiya Fatakwal ko wata jiha ko bakin coci ya yi bara, to fada min yadda Naira 6,500 za su cika masa ido. Wani yana bara ne saboda babu,wani kuma ba haka ba ne. Yanzu gwamnati ta dauki ’yan Hisba kuma ta yi musu duk abin da ya dace, ta dauki mutum 250 kuma za a ba kowane babur, muna jiran Majalisar Jiha ce kawai ta zartar dokar ’yan Hisba su fara aiki, amma muna ba su alawus kafin a fara aiki da zarar sun fara kowane almajiri da yake yawo kan titi za mu kama shi a hukunta shi. Kodai mutum ya koma makarantarmu ko ya zauna gidansa dole ne dai a daina bara.
Aminiya: Fiye da shekara biyu da hadewar kungiyar Izala wuri daya ko kana ganin an samu nasarar hadewar?
Mai Tafsiri: Hadewar kungiyar Izala ya samar da nasara, domin kafin haduwar in mun zo za mu dauki malamai sai mun sha wahala gudun kada mu yi wa wani bangare laifi. Amma a yanzu da kungiyar ta zama daya mukan dauki wanda muka ga ya dace, abu ya yi kyau tunda abu guda ne Shaidan ne ya raba kuma yanzu an hade.
Aminiya: Yallabai a halin yanzu kujera biyu ce kake kanta wato Kwamishina da kuma mukaddashin shugaban hukumar ilimi bai-daya, me zaka ce kan maganar da ake yi a gari cewa ilimin firamare yana ja baya duk da ana cewa ana tallafa masa?
Mai Tafsiri: To ka gyara maganarka ba ja baya ya yi ba, sai dai ka ce yana nan yadda yake, tunda kashe shi aka yi fiye da shekara goma. Fada min yadda za ka gyara shi cikin shekara daya ko biyu. Sa’annan a wasu wurare an san ya canja, misali koda muka je makarantar Gidan Sallau ba su da kujera 50, yau ka je makaratar ka ga me ke ciki, ka je duk wata makaranta da ke cikin garin nan ka gani. Sa’annan duk wata muna ba shugaban makarata Naira dubu biyu ya sayi alli, kuma mun san aiki ya inganta don inda aka fito malami ko shugaban makaranta sai su yi mako biyu ba tare da sun shigo makarata ba. Yau ba wani shugaba ko malami da ke mako daya bai shiga makarantarsa ba. Dubi ajujuwan da muka gyara, ba a samun gyara lokaci daya, duk da firamaren da Gwammna Wamakko ya kare a lokacin da muka zo kowa kasa yake zaune, to yanzu ka je makarantar ka gani yaro nawa ke zaune a kasa? A yanzu mun gama da cikin gari mun fara a kauyukka su ma za mu inganta su sosai. Kowace karamar hukuma za mu kai mata kujeru dubu don a fara da su, sai a hada da wadand ake da su a makaratar mu gani. Koda muka zo akwai makarata 1,965 da masu zagaya su mutum dubu amma ba a aiki, kuma abin takaici masu zagayen wasu ko ‘a’ ba su iya rubutawa, a lokacin da wasu jami’ai suka zo tantance su. Mutane sun gano wani mai zagaye ko karatarwa bai kamata aba shi ba, amma shi ne sufabaiza bai san komai ba, to yanzu halin da muke ciki an yanke su sun koma 500, wadannan su ne za mu raba wa makaratunmu bayan mun kara horar da su. Abin da muke so mutanenmu su yi shi ne su kula da amana da gaskiya. An gyara albashi bayan mun cire bara-gurbi daga cikinsu duk inda ka ga malami yana cikin farin ciki. Lallai mun iske ilimi cikin matsala, yanzu an hau matakin gyarawa.
Aminiya: A karshe me ya kawo tsaikon biyan malaman firamaren Jihar Sakkwato ariya dinsu?
Mai Tafsiri: Yadda ka san an samu tsaikon gyara albashi haka ne aka samu wannan tsaikon, misali a garin Shagari watan da ya gabata da muka sanya kwamitin bincike sai da muka samu jabun malamai 120, to haka kawai sai ka kwashi kudi ka ba mutanen banza da ba su yin aiki? Mun umarci shugabannin makarantu su kawo mana sunayen malamai har yanzu ba su kawo ba, da zaran sun kawo muka tantance, to za mu biya su, in yau suka kare aikinsu to a shirye muke mu biya.