Wigan Athletic ta sallami kocinta Kolo Toure bayan ya buga wasa tara ba tare da kungiyarsa ta samu nasara ba.
A watan Nuwamba ne aka nada tsohon dan wasan Arsenal da Manchester City a matsayin kocin da ya maye gurbin Leam Richardson.
- Koriya ta Arewa ta zargi Amurka da rura wutar yakin Rasha da Ukraine
- NRC ta dakatar da zirga-zirgar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
Sai dai maki biyu kacal Wigan ta samu a cikin wasa bakwai a gasar Championship.
“Matakin mai wuya ne amma hakan ne kawai zai bamu damar ci gaba da kasancewa a gasar Championship a kakar wasa mai zuwa,” in ji shugaban Wigan Malachy Brannigan.
BBC ya ruwaito Brannigan na cewa, “Ina godiya ga Kolo saboda aikin da ya yi tare da mu.”
Toure ya kasance mataimakin Brendan Rodgers a Celtic da kuma Leicester kafin Wigan da dauke shi a cikin watan Nuwamba.