Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fara shirye-shuryen fid da sabon suna, da kuma nau’o’i da tsare-tsaren da za su taimaka mata a rabon rigakafin cutar Kyandar Biri a kasashen da ke fama da ita.
Shugaban hukumar, Dokta Tedros Ghebereyesus ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar ranar Talata a hedkwatar hukumar da ke Geneva.
- Babu me yi wa Buhari katsa-landan a mulkinsa — Fadar Shugaban Kasa
- Babu me yi wa Buhari katsa-landan a mulkinsa — Fadar Shugaban Kasa
Ya ce WHO na hada hannu da abokan huldarta a yunkurinta na fitar da tsare-tsaren.
Ya kuma ce yanzu haka hukumar ta wallafa ka’idojin rigakafin cutar, tare da shawarwari ga gwamnatoci dangane da gano masu dauke da ita da kuma yadda za a magance ta.
A nasa bangaren, kwararren masani a bangaren cutar Kyanda na hukumar, Dokta Rosamund Lewis ya ce wayar da kan mutane kan hadarin cutar abu ne da ya zamo dole a yanzu.
Don haka ya shawarci al’ummar kasashen da ke fama da annobar, su tabbatar da wadanda ke dauke da ita sun kebe kansu, don gudin yada ta ga iyalai da makusantansu.
Dokta Lewis ya kuma ce duk da cewa a wasu lokutan cutar kananan alamu da suka da raunin fata take bayyanawa, duk da haka wani zai iya dauka a sati biyun zuwa hudu.
“Muna sane da cewa killace kai na tsawon lokaci abu ne mai wuya, amma yana da matukar muhimmaci ayi hakan muddin ana son rage yaduwar cutar. A mafi yawan lokuta mutum na iya killace kansa a gida ba dole sai a asibiti ba,” inji shi.
To sai dai Kwararren masanin ya ce ya zuwa yanzu ba su kai ga gano ko wanda ke dauke da cutar amma alamunta ba su bayyana gare shi ba zai iya yada ta ga wani ko kuma a’a.