✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

WHO ta ayyana Kyandar Biri a matsayin babbar barazana ga duniya

Mutum fiye da 17,000 ne ake zargin sun kamu da cutar a kasashe 75.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana cutar kyandar biri a matsayin babbar larura mai bukatar kulawar gaggawa ta duniya.

Wannan ayyanawa ita ce matakin ankararwa mafi girma da WHO ta dauka sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar.

An bayyana matakin ne bayan kammala taron gaggawa da kwamati kan cutar ya gudanar a Asabar din nan.

a cewar shugaban WHO Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus, mutum fiye da 17,000 ne ake zargin sun kamu da cutar a kasashe 75, inda ake samun karuwar masu harbuwa da ita a Yammaci da Tsakiyar Afirka tun daga farkon watan Yuli.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutum biyar.

Matsayin Hukumar shine hadarin cutar yana matakin da za a iya bayyana shi a matsayin matsakaici a shiyoyi 5 da ke duniya amma kuma banda yankin Turai wanda matsalar ke da girma.

WHO ta ce kashi 98 na wadanda suka harbu da cutar ’yan luwadi ne da kuma masu neman maza da mata a lokaci guda.

Ghebreyesus ya bukaci kasashen duniya da suyi aiki tare da al’ummomin dake neman maza domin samar da bayanan da zasu kare su daga harbuwa da cutar.