✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Waye sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero?

Sa’o’i bayan tube Sarki Sanusi II, aka nada Sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarki Ado Bayero . Muhimmman abubuwa…

Sa’o’i bayan tube Sarki Sanusi II, aka nada Sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarki Ado Bayero .

Muhimmman abubuwa game da Sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero:

  • Aminu Ado Bayero ya zama sarki na 15 a jerin Sarakunan Fulani na Kano.
  • Shi ne aka fara zaba a matsayin Hakimin Nasarawa, kuma mukamin Danmajen Kano wanda mahaifin shi Sarki Ado ya nada.
  • Ya rike mukamai a Masarautar Kano da suka hada da: Turakin Kano da Dan Buran da Sarkin Dawakin Tsakar Gida da kuma Wamban Kano.
  • Shi ne sarkin sabuwar masarautar Bichi da Gwamna Ganduje ya kirkira a shekarar 2019.
  • Shi ne da na biyu babba a maza ga marigayi Sarki Ado Bayero.
  • Ya yi karatun digirinsa a bangaren aikin jarida a jami’ar Bayero ta Kano.