✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wayar baturen da ta bace a Ingila ya gano tana Najeriya bayan wata guda

Na rasa wayata kirar iPhone wata daya ke nan yanzu a Liverpool.

Wani bature dan Ingila ya bayyana yadda ya gano wayarsa a Najeriya bayan wata guda kacal da ta yi batar dabo.

Baturen mai suna, Darren, ya bayyana afkuwar wannan lamari ne a shafinsa a Twitter.

Cikin mamaki mutumin ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan wata daya da batan wayarsa a birnin Liverpool amma kuma da ya yi bincike ta manhajar iCloud sai ya gano cewa a halin yanzu wayar tana Jihar Edo a Najeriya.

Ya dai sanya bayanan da ya samo kai tsaye a shafinsa na Twitter domin ya shaida wa mutane inda wayar tasa take a wannan lokaci.

“Na rasa wayata wata daya ke nan yanzu a garin nan…, yanzu ina shiga iCloud dina sai nake ganin cewa wayar tawa ta tafi hutu Najeriya,” a cewar Darren.

Domin samun labaran Aminiya da dumi-duminsu a shafinmu na Twitter ku latsa nan:

Kada ku manta ku danna alamar ‘Follow’ domin samun labaran a kan lokaci. Mun gode.