✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Watsattsaken wasikar waskiya (3)

Magabta na taron dangi ’Yan kore na kada musu gangi Don su jefa jama’a kangi Har ai ta kugi Waasikun buga duga-dugi Sun yi kwashi-kwaraf…

Magabta na taron dangi

’Yan kore na kada musu gangi

Don su jefa jama’a kangi

Har ai ta kugi

Waasikun buga duga-dugi

Sun yi kwashi-kwaraf

Suna kakaf-kaf

Don yi wa lalita karkaf

Sunkurun saraf na sadaf

Ai ta sallalamin aahaf af!

Caraf

Caf-cacaf

Sadaf

Sadaf

Daf-da-daf

’Yan dabarbaru

Dundumin dubarudu

dumamen tuwon Dudu

Toye-toyen dandaudu

ki-gudu yai musu kuru-kuru

Ba tsaro

Sai tsoro

Ala-koro

Jiki ai masa horo

Dattijo fasa taro

Marsa goriyar goro

Alawar biki a daro

Mata sun iya kada bambaro

Malam ya zauna a soro

Almajirai sun hallaro

Koyi ka koyar

Komai ka diba ka amayar

Dukiya ce an kaa sarayar

Hankalin kowa sun tayar

Aniyarsu sai a mayar

berayen taska

Sun wawushe turaka

Sun zame wa kasa kaska

Sai an kankare su da aska

A ingiza su su sha faska

Baba-Ojon gada-gada

Burgar tada kan adda

Juyin aya takadana

’Yan mata sun iya gada

barambarama tai gargada

Wa ya jefa mu cikin duhu

Har wasu ke ta ihu

A sana’a an rasa taro da ahu

A kara kaimin dinke buhu

An yi  batan rike runhu

Hakin numfashi da huhu

Girkinmu an sauke daga murhu

Daushe na nan a huhu

Santi ya sa su tsalle da ihu

Nauyinsu huhun ma’ahu

Baba-Ojo mai gonakin Otawa da Baban-gada-gada da ke kan tsuanin birnin Mina-mina can a Jihar Ni-na-ja, sun yi taron dangi, har ana kada musu gangi, wai don su ji dadin tuntsurar da Baban-burin-huriyya da ke jan ragamar Haurobiya, shi ya sa suka yi masa tsiwwa da tsiya-tsiya. Dadin lamarin dai wadannan jiga-jigan jigatan al’ummar kasa, sun sha yi wa juna TAHO-MU-GAMA, wanda duk yake inkarin wannan batu to sai ya duba mujallu da makalu don tantance yadda lamarin yake ba tare da ce-ce-ku-ce ba. Mujallar ‘’YAR CIKIN GIDA a dubu katramin lauje da sili da karamin lauje ta taba yin bayin shirin MAJIGIN HAUROBIYANA.

’Yar’didin Kekere, tsohuwar shagabar kasuwar ririta jaririn jari a kasar Haurobiya ta tabbatar da cewa Baba-ojo na da hannu dumu-dumu a kumbiya-kumbiyar kafa kamfanin TIRENSU-AKWAI-KWAF, inda ya mallaki MAKAUNIYAR AJIYA; a kamfanin DUHUNDUNdUMDURUNdUM kuwa an ruwaito yadda gwamnatinsa ta salwantar da Dalar Hauron Amurkawa sili da manuniyar sama wajen samar da kARFIN MAGAWATA kofar hanci da ya yi wa Haurobiyawa shigar hanci da kudundunen batnci ga kasa. Sannan a zamanin mulkin mulaka’u na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge aka tsuwurwurta haramben HALIN-BURTU: A bADDA KAMA, A YI bARNA, uwa-uba ga BASAUSSUKAN WUNI-WUNI irin na ’YAN UWAN DA BA SU DA WANI, masu BARGAR DAWAKIN SAMFARERA DA FADAR kURkURIDON HONDA da makamantansu.

Shi kuwa BABAN-GARGADA, ya yi gada-gadar dora Haurobiya kan turbar turka-turkar jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, har miyagu suka ji dadin yin koto, babu wanda ya daga musu kara, sai ma manya da suka yi musu kara, shi ya sa ba ku ji wani ya yi musu kwarmato ba. Kuma shi ne dai ake ta dora azargagiyar zarge-zarge a kansau, kan yadda aka salwantar da gwagwabar ribar da kasar ta samu sanadiyyar ARTABUN YANKIN TEKUN PASHA, yayin da ya yi washa-washa, mu kuwa aka bar mu muna ta assha-assha, domin an mayar da mu taron sususu da shashasha..

Haurobiyawa ku yi wa kanku kirdado, ku fito dododo, don bukatar ganin shagabannin al‘umma sun yi zubeben kwarya kan tabargazar da suka tafka da ayyukan alherin da suka aikata, ta yadda za a rairaye- a tankade tsakanin TSABA DA TSAKUWWA. Mutumin kwarai an sanshi sarai; mara kirki sai a taka masa burki, don ka da ya tattago miyagu su zo, su cigaba da yi mana dungu, su yi ta jin dadin taka rawar kidin kalangu.

Mun dai fasko masu CIN KWALAR CACUMAR CUMUIMIYAR CIN CA’AMMAS, wadanda suka kyale talaka dbusasshen tuwo kADAGAS, ya yi ta tauna kURUS-kURUS!

Sai kuma masu WARWASAWAR WAWAR WASOSON WASA-WASAR WAFCIYAR CIN GURSA GAMI DA MASA a zabi-sonka na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa, ba lamarin da ke gaban Baban-burin-huriyya ko Baba-Ojo ko Baban-gada-gada ba. Haurobiyawa kacokam za su yanke wa kansu hukunci, matukar dai an kauce wa fafutikar ci-mu-ci, a daura damarar kwatar ’yanci, don ka da a yi butulci, ta yadda al’umma za ta fice daga kunci. Kowa ya yi abin da ya kamace shi sai kasa ta yi ta bunkasa. Idan kuwa aka ci gaba da yin jimurda, to bangarorin da ba sa ga mesa da juna, kowa na tayar da kwanjin nuna shi ba kanwar lasa ba ne ba. Baba-Ojo dai ya yi JUYIN AYA, MASAKIN AYA TAKAdANdA, har ta kai ga a wasan dandali ya zarta ’yanmata iya GAdA, in dadi ya yi sai sai ya rangada guda, tunda yana da masnaiyar yadda suka sanya Haurobiyawasuka dandanin kuda. Wanan dai ita ce babbar JIMURdA a dama-dama da kurda-kurdar wasan Samson siya-siya a siyasar kasar Haurobiya. Domin har yanzu muna nan a bagiren DAMO-DA-KURA-DAdIYYA. A dai yi jimirin baje na-mujiya kan TAFIYAR TSUTSAR TURKA-TURKAR TAKUN SAkAR TALASURUN TUZURUN MUZURU!

Lallai Hauroibiyawa a jajirce wajen ganin an yi mai yiwuwa wajen sauke nauyin da ya rataya a kan kowa,musamman kan al’amuran da suka jibinci TARAIRAYA DA BIYAYYA. Haurobiyawa, a kiyayi daka wawa ko kokowa ba kakkautawa. Sai mu nuna wa juna SOYAYYA a daukacin fadin TARAYYA, kai har ma mu karade daukacin FAdIN IFIRIkIYYA, ta yadda a kowace ALkARYA mu zamto ’YA’YA babu baren da ake nuna wa kIYAYYA. Ita kuwa gwmanati ta tallafa wa rayuwar al’umma, tare da fadakarwa kan al’amuran da ke wakana a kasa, sai a ga kowa ya kara himma, don gudun kada a  ci gaba da tafka TA’ASA A KWANON TASA, al’amarin da ke haifar da SA-IN-SA a tsakanin shugabanni da al’ummar kASA.