✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata tsohuwa

Wata mota ce ta debo jama’a, ciki har da wata tsohuwa. Ana cikin tafiya sai tsohuwa ta ce: “Jama’a idan an zo Kaduna a fada…

Wata mota ce ta debo jama’a, ciki har da wata tsohuwa. Ana cikin tafiya sai tsohuwa ta ce: “Jama’a idan an zo Kaduna a fada min.” Jama’ar mota suka ce to. Ana tafiya sai tsohuwa ta ce: “An zo Kaduna ne?” Sai jama’ar motar su ce a’a, kai har aka wuce Kaduna. Sai tsohuwa ta ce an zo ne? Jama’a suka ce har an wuce, sai ta tada jijiyoyin wuya, cewa sam ba ta yarda ba sai an koma Kaduna. Jama’a suka yi ta ba ta hakuri amma ta ki yarda, har sai da aka dawo Kaduna. Ana zuwa sai ta tsaya ta ciro kwayoyin Paracetamol a jikkarta ta sha, ta ce: “Mu juya mu ci gaba da tafiya, dama likita ne ya ce idan an zo Kaduna in sha maganin.”