Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta buga a ranar Litinin da ta gabata, ya daga min hankali sosai a kan yadda muke kashe kawunanmu saboda gaggawar da muke yi mu tara abin duniya ta hanyar nuka kayayyakin marmarin da muke nomawa, irin su mangwaro da ayaba da filaten da sauransu.
Binciken jaridar ya nuna cewa yadda ake nukaka kayayyakin marmarin da wani sinadari da ake kira calcium carbide wanda ake amfani da shi wajen yin walda don hanzarta nunar wadannan kayayyaki yana jawo cututtukan daji (kansa) da na koda da na hanta da kuma na zuciya. Wadannan cututtuka kuwa kowa ya san masu saurin kisa ne ko masu wuyar magancewa ga talakawa masu karamin karfi.
Rahoton ya ruwaito Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC) tana gargadin ’yan Najeriya a baya-bayan nan su guji sha ko cin kayayyakin marmarin da aka nuka da wannan sinadari na calcium carbide.
Binciken wakilan jaridar a Kasuwar Kayan Marmari ta kasa da ke Zuba a hanyar Abuja zuwa Kaduna da takwararta ta Mararraba da ke hanyar Abuja zuwa Nasarawa wadanda su ne manyan kasuwannin kayan marmarin da suke samar wa Yankin Birnin Tarayya (FCT), kayayyakin marmari, ya gano ana matukar amfani da wannan sinadari wajen nukaka kayayyakin marmarin, ya alla manoma su yi hakan ko ’yan kasuwa su yi hakan domin kayayyakin su nuna da wuri su sayar ga jama’a.
Wakilan jaridar da sun je kasuwannin ne a matsayin masu son sayen abarba da gwanda da ayaba ko filanten da ake kawowa daga jihohin Edo da Ondo da Kwara da lemo da mangwaro da galibi aka fi kawowa daga jihohin Benuwai da Nasarawa, sai kankana da galibi ke fitowa daga jihohin Arewa masu nisa, kuma sun gano cewa abu ne mai wahala a samu kayayyakin marmarin da ba a nuka da wannan sinadari na calcium carbide ba a kasuwannin biyu. An ma shaida musu cewa in dai ba ’yan kalilan da suka nuna da kansu a daji ba, zai yi wuya a samu wanda ba a sanya masa wannan sinadari ba.
Ku,a ’yan kasuwar kayan marmarin da dama su da kansu suka tabbatar da cewa sinadarin yana da mugun hadari ga lafiyar dan Adam, amma duk da haka sun tabbatar manoma da su kansu ’yan kasuwar suna amfani da shi wajen tilasta kayayyakin su nuna cikin hanzari.
karewa ma wakilan jaridar sun iske masu sayar da sinadari suna ta gudanar da harkarsu a wurare da dama suna tallata sinadarin ga wadanda suke sayen kayayyakin da ba su nuna ba. daya daga cikinsu mai suna Misis James da ke sayar da sinadarin a inda ake sayar da ayaba da filanten ta ce: “Sinadarin yana da mugun hadari. Zai iya hallaka dan Adam.” Kuma da aka tambaye ta yaya take tsare ’ya’yanta daga isa gare shi, sai ta ce: “Ba na kai shi gida. Nakan ajiye shi ne a cikin shagon.” Kuma ta bayyana yadda ake amfani da shi cewa ana iya watsa shi a kan kayayyakin marmarin sannan a wanke shi, ko a sanya shi a tsakiyar kayan marmarin da aka tara sai a lullube su kuma wannan ne hanyar da ta fi saurin nunar da kayan. Sai dai ta ce an fi amfani da sinadarin wajen nuka ayaba da mangwaro, amma ba ta da masaniya ko ana amfani da shi wajen nuka lemo da abarba.
Hakika ba ma sinadarin yin walda na calcium carbide kadai ba, manoma da masu sayar da kayayyakin amfanin gona da na marmari suna matukar jefa rayuwar jama’ar kasar nan a cikin hadari ta hanyar amfani da sinadarai daban-daban da suke iya jawo cututtukan da suke hallaka rayuka.
Fiye da shekara 25 da suka gabata ni da kaina na taba ganin yadda wadansu masu sayar da ayaba a Kasuwar Muda Lawal da ke Bauchi suke amfani da fiya-fiya wajen nuka ayaba a dirom-dirom. Sannan sau nawa ake amfani da maganin kashe kwari wajen adana wake sai kawai mutum ya dauko ya kawo shi kasuwa ya sayar mutane su je su yi amfani da shi, masu mutuwa su mutu, masu tagayyara su tagayyara?
Babban abin bakin ciki, kusan duk wani nau’in abinci bai kubuta daga amfani da magunguna da sinadaran da suke da hadari ga rayuwar jama’a ba. Masunta da dama sun rika amfani da sinadarin Gamalan 20 da danginsa a ruwan da suke yin su domin galabaita kifin da suke son kamawa, a karshe mutane su sayi kifin ya yi musu illa da sanya rayuwarsu a cikin hadari ba tare da sun sani ba.
A shekara biyu da suka gabata kasashen Turai da dama sun haramta sayen ridi da kifi da wake da wasu kayayyakin abinci daga Najeriya bisa kukan cewa ana sanya musu guba. A karshe dai an gano cewa a kasar nan hatta shinkafa ba ta tsira ba, inda ake zargin manoma da yi mata feshi da sinadarai domin ta hanzarta bushewa a yanke a sarrafa ta a sayar ga jama’a. Ridi ma haka ake yi masa feshin don ya gaggauta bushewa a raba shi da gona a kawo kasuwa a sayar!
Irin wannan gaggawa da ’yan Najeriya suke yi don ganin duk abin da suke yi ya kosa a wani takaitaccen lokaci ne ya sa ake amfani da guba iri-iri ana tilasta wa amfanin gona saurin nuna a karshe kuma a jawo wa jama’a cututtukan da ba a san kansu ba. Idan manomi yana ganin riba ne a wurinsa kuma ba shi zai ci kayan ba, don haka kowa ma ya mutu ko ya tagayyara, to kada ya manta masunci ma yana yin haka, in ya kubuta daga nasa ba zai kubuta daga na wani ba. Haka lamarin yake a wurin shi ma masuncin da sauransu. Don haka ya kamata ’yan Najeriya su cire dabi’ar nan ta yin komai a gaggauce da bukatar samun dukiya cikin gaggawa da sauri. Su daina amfani da ire-iren wadannan sinadarai suna jefa rayuwarsu da ta jama’ar kasar nan a cikin hadari.
Yanzu dai muna ganin yadda muke fama da cututtukan da ba a san kansu ba, ake ta samun karuwar mace-macen farat-daya, wannan kuma yana da alaka da ciye-ciyen kayayyakin marmari da na abinci masu dauke da guba irin wadannan. Masu iya magana dai sun ce yi wa wani yi wa kai ne. Don haka mu daure mu daina sanya rayuwar jama’armu a cikin hadari ta amfani da irin wadannan nau’o’in sinadarai da suke zama gubar da ke jawo mana cututtuka masu galabaitarwa ko kisa farat-daya. Wannan ba abu ne da shugabanni za su iya hana mu ba, mu da kanmu ne za mu hana kawunanmu aikata wannan son zuciya da muke yi. Kuma akwai bukatar malamai da limaman addinai su tashe tsaye wajen fadakar da jama’a kan wannan muguwar dabi’a ta amfani da guba wajen nuka kayayyakin abinci da na marmari da wadansunmu suke yi a karshe su jawo mana bala’i.