✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wata mata ta yi karar tsohon mijinta saboda auren babbar kawarta

Mun yi aure ba jimawa amma ba mu tare a kowane gida ba har tsawon watanni biyu.

Wata mata ‘yar kimanin shekaru 25 mai suna Firdausi Musa, ta maka tsohon mijinta, Sa’idu Abubakar, a gaban wata kotun shari’a da ke Jihar Kaduna bisa laifin auren babbar aminiyarta.

Firdausi, ta bakin lauyarta, Madam Zainab Murtala, ta ce wanda ake tuhumar ya kuma mika akwatuna da kayan lefen aurenta ga sabuwar matarsa.

Ta shaida wa kotun cewa, “Mun yi aure ba jimawa amma ba mu tare a kowane gida ba har tsawon watanni biyu. Otel-otel kawai yake kamawa mu hadu.

“Ana tsaka da haka ne kawai sai ya sake ni, kuma ya auri babbar aminiyata; har da hada mata da dukkan kayayyaki na, ciki har da tufafi.”

Firdausi ta roki kotu da ta taimaka ta kwato mata dukkan kayayyakin da ya yi mata na aurenta da wadanda ta siya a lokacin da ta je Umarah.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito Firdausi tana shaida wa kotun cewa ita ba ta taba neman ya tsinka igiyar auren da ke tsakaninsu.

A nasa bangaren, Sa’idu Abubakar wanda ake karar ta bakin lauyansa, Abubakar Sulaiman, ya musanta bai wa tsohuwar matarsa ​​kyautar kayayyakin aure kamar yadda ta yi ikirari.

Sai dai Alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Agusta.