✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wata mata ta kashe kanta ta hanyar rataya

An tsinci gawar wata mata da ake zargin ita ce ta rataye kanta a cikin wani kangon gini da tsakar dare. Lamarin ya faru ne…

An tsinci gawar wata mata da ake zargin ita ce ta rataye kanta a cikin wani kangon gini da tsakar dare.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da tsakar dare a yankin Idokpa na Karamar Hukumar Uwhunwinde ta Jihar Edo.

A safiyra Juma’a ne mazauna unguwar suka tsinci gawar mata a rataye a jikin rufin kangon.

Amma wani dan unguwar ya yi zargin kashe ta aka yi, saboda a cewarsa, “Tsayin rufin ginin ya fi na kayan da ta rataye kanta da shi sosai, babu yadda za a yi daga kasa ta iya rataye kanta da kayan a jikin rufin ginin.”

Mazauna yankin dai sun ce matar ba ’yar unguwar ba ce kuma babu wanda ya san sunanta ko daga inda ta fito.

An tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, Bello Konongs, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi karin bayani ba.