✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata kyanwa

Wani mutum ne matarsa ke da kyanwa, kullum ta dame su da barna. Wata rana sai ya dauke ta, ya yi tafiya mai nisa da…

Wani mutum ne matarsa ke da kyanwa, kullum ta dame su da barna. Wata rana sai ya dauke ta, ya yi tafiya mai nisa da ita cikin daji da motarsa. Ya aje motar, ya dauki kyanwar ya yi tafiya mai nisa da ita cikin dajin nan, ya jefar da ita. Ya kama hanyar dawowa sai ya yi makuwa, ya rasa inda ya aje motar. Tun safe yake tafiya har La’asar bai kai ga inda ya aje motar ba, sai ya buga wa matarsa waya, ya sanar da ita halin da yake ciki. Matarsa ta ce: “Ai kuwa bayan tafiyarka da awa biyu sai ga kyanwar ta dawo gida.” Shi kuwa sai ya kara rudewa, ya ce wa matar: “Ba kyanwar waya mu yi magana da ita”
Daga Lawali Shehu Tsafe 08091573703