✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wata budurwa ta yanke mazakutar saurayinta

Ana zargin wata budurwa mai suna Brenda Baratti da yanke mazakutar saurayinta da almakashi a kasar Ajantina. Barattini mai shekara 26 a rayuwa ta ce…

Ana zargin wata budurwa mai suna Brenda Baratti da yanke mazakutar saurayinta da almakashi a kasar Ajantina.

Barattini mai shekara 26 a rayuwa ta ce aikata wannan aika-aikar ne saboda tana zargin saurayin na ta da nuna wa abokansa faifan bidiyo yadda suke saduwa a gida.

Yanzu haka an tasa keyar ta zuwa gidan kaso kafin a kammala shara’ar, sannan shi kuma saurayin mai suna Sergio Fernandez yana asibiti inda yake ci gaba da jinya.

“Na yanke masa mazakuta, amma ba baki dayan mazakutar na yanke ba, amma dai na ji masa rauni, inji ta.”