Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato.
Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita.
Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari.
- ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno
- Turji: Gwamnatin Sakkwato ta ba da sharadin sulhu da ’yan ta’adda
Wani mazaunin yankin da ke sana’ar sayar da kifi ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, kuma mutum daya ne kadai ya samu rauni a motar.
Jami’in Wayar da Kan Jama’a na Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a Jihar Filato, Yakubu Lonsan, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya kara da cewa hukumar tana yin duk abin da ya kamata domin kawar da motar da ma cunkoso a wurin da abin ya faru.