✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu mutum 4 da suka harbi Bafulatani makiyayi a Ogun sun shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kame wasu mutum hudu da ake zargin su da harbin Bafulatani makiyayi mai suna Abubakar Idris, a lokacin da…

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kame wasu mutum hudu da ake zargin su da harbin Bafulatani makiyayi mai suna Abubakar Idris, a lokacin da yake kora shanunsa a garin Ijebu Ode ta shiyyar kauyen Olugbo da ke yankin Idea.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa wadanda ake zargin sun hadar da: Ogunseye Funso da Omniyi Benj  sun yi wa makiyayin mummunan rauni a kafa,

DSP Abimbola, ya kara da cewa, “Jami’an mu sun far masu ne bayan da suka yi aika aikar a ranar Larabar makon jiya sai suka gudu suka boye a mafakar su inda anan muka kame su bayan kwana biyu da faruwar lamarin, zuwa yanzu ana kula da lafiyar makiyayin a asibiti kuma Kwamishina ‘yan sandan Ogun Kenneth Ebrimson, ya bada umarnin kai wadanda ake zargin sashin binciken manyan laifuka kafin daga bisa ni a gurfanar dasu a kotu.