✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasikar Obasanjo farmakin karnuka ne ga Shugaba Jonathan

Wasikar Obasanjo ta tada kura a fagen siyasar Najeriya, duk da wasu jami’a suna kare gwamnati da cewa zargi ne, kuma ma cin amanar kasa…

Wasikar Obasanjo ta tada kura a fagen siyasar Najeriya, duk da wasu jami’a suna kare gwamnati da cewa zargi ne, kuma ma cin amanar kasa ne. Yayin da ake ganin dama ce ta fadar shugaban kasa ta nuna gaskiyar ta, game da halin da ake ciki, ta karyata wasikar, amma abin da kamar wuya domin wasu bayanan ana ganinsu karara!
Wannan wasika ta zamo tamkar farmakin karnuka a tsakanin tsohon Shugaban kasa Cif Obasanjo da Jonathan Goodluck mai ci a yanzu. daukacin miyagun laifukan da Obzsanjo ke zargin Jonathan da tafkawa, shi ya taba aikata irinsu. Wannan al’amari dai ya rage ga ’yan Najeriya su dauki mataki a kan shugabanninsu, don gudun kada su yi yadda suka ga dama da kasar nan.
A fili yake cewa satar da aka yi da wadda aka kawar da kai a wannan mulkin ta yi yawa, kusan an tsiyata kasar domin babu komai a asusun ajiyar kasar na kasashen waje, sannan gwamnatin ta gaza yin komai ga kudin ‘yan fensho da aka cinye, ga maganar tallafin man fetur da wasu mutane kalilan suka wawushe, kuma ga bayanin miliyoyin da aka fitar don a sayi motoci biyu ga minista daya, sannan talauci sai karuwa yake yi.
Katobarar da Obasanjo ya yi ta samu karbuwa a wajen ’yan adawa wanda hakan ya sa aka fara sabon yunkurin ganin an tsige Jonathan daga karagar mulki, musamman ganin dama duk abin da Obasanjo ya rubuta a wasikar ba sabo ba ne, kowa ya san batun!
Kowa ya san wannan gwamnatin ta gaza, musamman idan muka kalli yadda rashin tsaro ya yi tabarbbarewar da bai taba yi ba a tarhinin Najeriya, ga cin hanci da rashawa wanda dama ana yi, amma ba a taba samun lokacin da ake neman cinye talaka ba, domin dama an cinye hancin!
Sannan sai maganar harkar ilimi, wanda abin kunyar da ya faru tsakanin gwamnati da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ya isa abin kunya a wasu kasashe, hart a kai ga shugaban kasar da kansa zai sauka, amma har barazanar korar malamai yake yi daga makarantu! Ka rasa wace irin kasa suke so su haifa?
Wasu manazarta na da ra’ayin cewa ba abin da ya raba Obasanjo da Jonathan sai don tsohon shugaban yana kokarin yin tasiri a gwamnatin sabon! Domin shi ma da manyan  Arewa suka goyi bayansa a 1999 ba wanda ya juya wa baya sai Arewa. Yayin da ya yi wa dimokuradiyya karan tsaye, ya kawo marigayi Umaru ‘Yar aduwa, wanda mataimakinsa Jonathan ya yi sa’ar zama sabon shugaban.
Za a iya cewa Jonathan magajin Obasanjo ne, domin kowanne daga cikin su ya yaki jam’iyyarsa, a zamanin Obasanjo sai da ya kori shugaban jam’iyya (PDP), ya nada wanda yake so, yanzu kuma yana gaba don tsarin da ya so dora Najeriya ya sauya! Kowa ya fifita kabilarsa a cikinsu, amma fifikon Jonathan ya yi yawa! Shi har rijiyoyin man fetur ya ba su kyauta, ba wai kari a kason kasafi ba.
Kuma a zamanin Obasanjo an kashe manyan mutane! Wasu ma wadandanda suka saba da shugaban kasa ne, ba tare da kama wadanda suka yi kisan ba, sai dai a yanzu da Obasanjo ya ce ya san akwai irin wannan shirin a wannan gwamnatin sai ya nuna inda ake ba maharban horo, kuma ya kawo takardar sunayen ‘yan siyasan da ake sa wa ido, wadanda ya ce za a kashe su dubu! Ko a kama Obasanjo a kai shi kotu don ya wanke kansa daga kazafin da yawa gwamnati, ina ganin haka ma mafita ce.
Duk da cewa wasu na yaba wa Obasanjo ganin har sai da ya mari Fasto a lokacin da aka yi wani rikicin addini a kasar, yayin da a zamanin Jonathan kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta zama kusan daya da gwamnatin, domin ba abin da za a yi ba tare da an bai wa Kiristoci fifiko ba, duk da cewa akwai ‘yan Arewa da Musulmi a majalisar koli, amma duk a banza.
Kuma idan za a yi yaki da cin hanci da rashawa dole a fara da kama Obasanjo, don ban da cin hanci da rahsawa da ya iske, ya cinye fuskar! Sai da ya halalta magudin zabe a siyasar Najeriya! kuri’ar talaka ta
bar aikin, shiga layin zabe ma bata lokaci ne. Ta yadda tun da Obasanjo ya hau kan mulki aka gaza gudanar da sahihin zabe a kasar!
Yayin da ya nemi zarcewa sau uku! Wani tsari da Jonathan yake son yi a sunan karo na biyu! Wanda duk da cewa ‘yan siyasa daga Arewa na ganin lokaci ne da mulki ya kamata ya dawo Arewa, amma rashin hadin kai da munafunci na iya ba Jonathan damar tabbatar da mafarkinsa.
A halin yanzu malamai, sarakuna da ‘yan majalisa suna da damar ceto kasar daga halin da ta fada, kuma take neman fadawa.  Domin idan aka bar mabarnata suna barna, barnar kara girma za ta yi! Kuma talakawa sun fi kowa shan wahala. Idan aka gaza yin komai Allah kadai ya san halin da talakawa za su shiga nan gaba.

Buhari Daure
Muryar Talaka
[email protected]
+2347035986444