✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasannin tashe a Kasar Hausa

Tashe a kasar Hausa wata dadaddiyar aláda ce ta Bahaushe wacce ake danganta ta da al’adunsa masu nasaba da addini. Irin wadannan aládu su ne…

Tashe a kasar Hausa wata dadaddiyar aláda ce ta Bahaushe wacce ake danganta ta da al’adunsa masu nasaba da addini. Irin wadannan aládu su ne wadanda suka samo asali daga tasirin da addinin Musulunci ya yi ga rayuwar Hausawa ta yau da kullum tun bayan da addinin musuluncin  ya zo kasar Hausa ta hanyar Larabawa fatake wadanda suka zo kasar Hausa tun wajajen karni na sha takwas.

Kamar yadda kalmar ta zo wato tashe, asalin wannnan wasa da samari da ‘yan mata suke aiwatarwa a cikin watan azumi ana yinsa ne da nufin  tasar da masu barci su tashi su yi sahur. Wanda kuma daga baya sai aka rinka gabatar da shi a duk lokacin da watan azumi ya kai kwana goma. Wato da zarar an gama goma ta marmari za ka ga da yamma ko da almuru ko kuwa da dare bayan an ci abinci kuma an gabatar da sallar asham samari da ýan mata suna ta karakaina suna aiwatar da irin tashen da suka shirya. Haka kuma wasan tashe wasan kwaikwayo ne da matasa suke aiwatarwa don su fadakar kuma su nishadantar da masu ibada wadanda suka sha yunwa da  kishirwa kuma suke bukatar hutu da raha.

Wani babban makassudin yin tashe shi ne yadda yake koyar da darussa da dama a kowane fanni na rayuwa. Ta yadda masu gabatar da tashen sukan yi kokarin kwaikwayon wata dabiá mai kyau ko marar kyau da wasu suke yi a cikin al’umma wacce ake son su gyara saboda muninta ko kuma su dore saboda kyawunta don ci gaban alúmma. Don haka a iya cewa tashe wata makaranta ce ta koyar da tarbiyya da aládar Hausawa.

A cikin wasannin tashe kuma har wayau akwai hannunka mai sanda ga shugabanni da magidanta da kuma malamai akan yadda suka saki hanya ko kuma yadda ya kamata su yi don shugabantar alúmmar da suke a ciki. Masu tashe kan yi shiga da ado da kuma Magana irin ta duk wanda suke son su kwaikwaya domin su samu isar da sakonsu ga alúmma. Haka kuma masu gabatar da tashe sukan bi gida-gida ko kasuwanni da kuma sauran wurare inda mutane ke taruwa su yi masu tashen, tare da gabatar da wakokin tashe a wani saín ma har da kida da rawa sukan hada. A yayin da su kuma masu kallo ko sauraron tashen ke basu kyaututtuka na kudi ko hatsi ko kuma wani abin marmari.

Tashe ya kasu kashi-kashi, misali  akwai tashe na ýan mata da kuma na samari. Anan ana nufin yara samari sukan ware tawagar sa’annin su sais u gabatar da nasu wasan tashen ba tare da cudanyawa da ýan mata ba, haka kuma ýan matan su ma sukan yi nasu. Kuma kowannen su ya sha banaban da juna. Wato irin wasan tashe da wakokin da ýan mata suke yi ya banbanta da na samari. Sai dai a wasannin tashe da dama da ýan mata ke yi sukan yi shiga irin ta maza. Wasu daga cikin wasannin tashe na samari sun hada da wasan Gwauro ya tsinke, sakan ni in ciwo dawo, mai kacaniya, ka yi rawa dan malam, dokin kara, da mace ba gaba da dai sauransu. Daga cikin wasannin tashe na ýan mata kuma akwai; Ga mairama ga Daudu, mai ciki, Asha ruwa, da sauransu.

Akwai kuma wasu nauín tashe da manya ke gabatarwa da dama wadanda akasari ana yinsu ne a fada da kuma gidajen masu hannu da shuni. Wasan tashe wasa ne wanda za a iya kirkira duba da irin kalubalen da alúmmar da ake ciki take fuskanta da yanayin faruwar wani muhimmin abu a shekarar da ake gabatar da shi.  Dukkannin masu gabatar da wasannin tashe kama daga yara da samari da manya sukan samu tarba mai kyau da kuma kyautuka daga jamaá ganin yadda alúmmar Hausawa suke sane da muhimmancin tashe ga al’ada ko rayuwar Hausawa. Musamman ma ta irin darussan da ake dauka daga wasannin na tashe.

Yadda ake gabatar da wasan tashe na ‘Sakan ni in ciwo dawo’

Wasan tashe na sakanni in ciwo dawo wasa ne da samari suke gabatarwa, a inda za su zabi daya daga cikinsu sai a tube masa riga ayi masa ado a jikinsa da farar kasa sannan a shafa masa bula a fuska. Daga nan kuma sai a samo igiya doguwa a daura masa a kwankwaso, sai wani ya rike igiyar ta bayansa. Su kuma sauran samari suna biye shi kuma wanda aka daura ma igiyar yana gaba suna shiga gida-gida. Inda da zarar sun shiga sai ya yi kokarin ya zabura yana son ya ruga ya shiga dakin da yake a cikin gidan da suka shiga yana fadin;

“Sakan ni in ciwo dawo.” Shi kuwa wanda yake a rike da igiyar yakan dage ya jawo shi baya sauran yara kuma suna bashi amsa suna fadar “dakin na gidanku ne?” haka dai zai dinga yi shi kuma wanda yake a rike da shi yana komowa da shi baya.

Darasi

Darasin da wannan wasan tashe yake koya ma yara shi ne yaro zai san cewa taba kayan da ba nashi ba laifine babba a cikin alúmmar Hausawa. Ta yadda ana nuna ma yara cewa ko da ma ace gidan danginka ne ko na wani na kusa da kai to ba ma wani abu da yake da muhimmanci ba ko da dawo ne wato fura wacce ka ke zaton kafi karfinta a wannan gida bai kamata ka yi gaban kanka ka sanya hannu ka dauka ba tare da masu gidan sun baka ba.