✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan share fage: Yau Najeriya za ta hadu da Kamaru

A yau Juma’a ne da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya, kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da takwararta ta…

A yau Juma’a ne da misalin karfe biyar na yamma agogon Najeriya, kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da takwararta ta kasar Kamaru da ake yi wa lakabi da Indomitable Lions a wasan share fage na neman hayewa gasar cin kofin duniya da zai gudana a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu.  

Wasan zai gudana ne a filin wasa na Godswill Akpabio da ke garin Uyo na Jihar Akwa Ibom.  Kawo yanzu Najeriya ce take samun tebur a rukunin B da maki 6 a wasanni biyun da ta yi sai Kamaru ke biye da maki 2 sai Zambiya mai maki daya sai kuma Aljeriya da ita ma ke da maki daya.

A ranar Litinin 4 ga watan nan ne Najeriya za ta bi Kamaru gida don yin wasa karo na biyu.  Wasan kuma zai gudana ne da misalin karfe 6 na yamma agogon Najeriya.

Tuni kocin Najeriya Gernot Rohr ya gayyaci zaratan ’yan kwallon da yake ganin za su kare martabar Najeriya a wasan yau, sai dai shahrarren dan kwallon Arsenal Aled Iwobi ba zai buga wasanni biyun da Najeriya za ta yi da Kamaru ba saboda raunin da ya samu.

Idan Najeriya ta doke Kamaru a wasanni biyun,  za ta hada maki 12 kenan da hakan zai ba ta damar hayewa gasar cin kofin duniya a Rasha, idan Kamaru ce ta samu nasara a wasannin biyu, to za ta hada maki 8 kenan da hakan zai ba ta damar ba Najeriya tazarar maki biyu kuma hakan zai jefa Najeriya cikin matsala.

Duk kungiyar da ta kasance ta farko a kowane rukuni biyar daga Nahiyar Afirka ce za ta haye gasar cin kofin duniya a Rasha.

Ana sa ran dubban magoya bayan kwallon kafa ta Super Eagles daga sassan kasar nan ne za su yi tururuwar zuwa filin wasa na Uyo don ganin yadda wasan zai kaya, kamar yadda wasu dubban magoya bayan kungiyar za su kalli yadda wasan zai kaya a akwatunan talabijin dinsu.

Tuni jami’an tsaro suka shirya tsaf don ganin sun bayar da kariyar da ta kamata a yayin da kuma bayan wasan.

Masana harkar kwallo suna ganin wasan zai yi zafi, ganin yadda manyan kasashen da ake ji da su a bangaren kwallon kafa a Afirka ne za su hadu don kece raini.  Najeriya dai ba kanwar lasa ba ce a bangaren kwallon kafa kamar yadda Kamaru take takama da zaratan ’yan kwallo da ke wasa a sassan duniya.

Fatarmu dai shi ne Allah Ya ba Najeriya sa’a kuma a yi wasa lafiya, a kuma tashi lafiya.