✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan MATCH4IDPS ya hadu da cikas saboda almundahanar tikiti

An zargi ’yan sandan da aka ajiye a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano don samar da cikakken tsaro a lokacin da ake…

An zargi ’yan sandan da aka ajiye a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano don samar da cikakken tsaro a lokacin da ake gudanar da wasan kwallon kafar MATCH4IDPS da cika lalitarsu ta hanyar yin almundahana a wajen bayar da tikitin shiga kallon wasan da aka yi a karshen makon da ya gabata.

Shi dai wannan wasa na MATCH4IDP an shirya shi ne tsakanin Qungiyar Qwallon Qafa ta Kano Pillars da takwararta ta African Legends wato kungiyar da ta hada ’yan wasa da suka fito daga kasashe daban-daban a fadin Afrika, da nufin wayar da kan al’umma game da halin da ’yan gudun hijira suke ciki a fadin kasar nan.

Sai dai wannan wasa ya gamu da cikas sakamakon karbar tikiti da ’yan sanda suka yi daga hannun magoya baya inda suka sake sayar da shi ga wasu mutane masu son shiga kallon wasan tare da karkatar da kudin ga lalitarsu.

Binciken Aminiya ya gano cewa an tara kimanin Naira miliyan 2.5 sabanin Naira miliyan 15 da aka sa rai za a samu a wasan.

A wani taro da aka shirya bayan kammala wasan, masu shirya wasan sun samu labarin cewa ma’aikatan gudanarwar filin wasan sun hada baki da wasu bata-garin matasa inda suka balle kofofi biyu na shiga filin wasan don ya zama mafaka ga almundanar da suka shirya yi yayin da a gefe daya ’yan sanda suka cika aljihunsu da kudin ’yan gudun hijira.

Mataimakin Manajan filin wasa na Sani Abacha wanda kuma shi ne Kodinetan masu kula da harkar tikiti Usaman Abba ya bayyana cewa ’yan sanda ba su taimaka wajen gyara al’muran ba sakamakon halin ko in kula da suka nuna a ranar wasan.

Duk da cewa bai yi karin haske game da batun da ake yi cewa wasu jami’ai sun sake buga tikitin ta bayan fage ba, amma wata majiya ta bayyana cewa tun da sassafe wani jami’in filin wasan ya karbi daya daga cikin tikitin inda ake ganin ya yi hakan ne da wata manufa.

Madam Abi Goodman ita ce kodinatar shirya wasan ta bayyana cewa abin takaici ne kwarai da gaske wasu mutane su yi kokarin sama wa ’yan gudun hijira dan abin da zai taimaka wa rayuwarsu, amma a samu wasu mutane wadanda su aka dora wa alhakin kula da tsaro su daka wawa a kudin ’yan gudun hijira wadanda ragowar yakin ’yan Boko Haram ne.

Aminiya ta rawaito cewa  a wasan na MATCH4IDPS Qungiyar wasan kwallon kafa ta Kano Pillars ita ce kan gaba inda ta lallasa takwararta ta African Legend da ci biyu da daya.

DSP Magaji Musa Majiya shi ne Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ya musanta wannan batu, inda ya bayyana cewa ba su samu wani korafi a rubuce ko da baki a kan hakan ba.

Sai dai Majiya ya bayyana  cewa a shirye rundunarsu take idan ta samu irin wannan korafi ta dauki matakin da ya dace a kan jam’ianta. “Ina tabbatar da cewa idan muka samu korafi daga wadanda suka shirya wasan ko ma’aikatan filin wasa na Sani Abacha to za mu gudanar da kyakkyawan bincike saboda mun san jami’anmu da muka kai wurin don samar da tsaro, kuma idan har mun same su da laifi za mu hukunta su daidai da laifinsu.”