✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan kwallon kafa ya taimaka wajen kawo zaman lafiya a Filato – Sunday Longbap

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Jihar Filato Honarabul Sunday Samson Longbap ya bayyana cewa babu shakka harkokin wasan kwallon kafa ya taimaka wajen kawo zaman…

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Jihar Filato Honarabul Sunday Samson Longbap ya bayyana cewa babu shakka harkokin wasan kwallon kafa ya taimaka wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Filato.  Sunday Samson  ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Aminiya.

Ya ce a da idan mutum ya zo babban filin wasan kwallon kafa  na Jos ba zai ga kowa ba, saboda tsoran da mutane suke yi. Ya ce amma da zuwan Gwamna Lalong ya ba wasan kwallon kafa da sauran wasanni muhimmanci, yanzu harkokin wasanni ya dawo a filin wasan na Jos, a kullum filin  yana cika makil da mutane.

A kullum mutane daga Bauchi da Gombe da sauran sassan Nijeriya suna cika filin wasa na garin Jos, hakan yana nuna  zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo a garin Jos.”

Ya yaba wa Gwamnan Jihar Filato kan kokarin da yake yi  na kammala aikin gina babban filin wasa na garin Jos da ke kan hanyar Zariya. Ya ce gwamnoni sun kai 12 da suka wuce a jihar nan, ba su kammala wannan aiki ba, amma gwamna Lalong da zuwansa sai ya dukufa kan kammala aikin gina wannan filin wasa.