✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wasan kawance: NFF ta bayyana ’yan wasa 30 da za su taka wa Najeriya leda

Mai horar da ’yan wasa na tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles, Salisu Yusuf ya bayyana sunan ’yan wasa 30 da za su buga…

Mai horar da ’yan wasa na tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles, Salisu Yusuf ya bayyana sunan ’yan wasa 30 da za su buga wasan kawance da Mexico da Ecuador

Gasar, wacce ,a a buga wasan ne a kasar Amurka za kuma ta hada da kyaftin din tawagar, Ahmed Musa da takwaransa Moses Simon.

Sunayen dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) ta fitar, sai dai har ila yau an kira Kyeftin din tawagar Ahmed Musa da takwaransa Moses Simon.

Super Eagles dai za ta fara buga wasan ne da ’yan tawagar Mexico ranar 28 ga watan Mayun 2022 a Jihar Texas ta Amurka.

Kazalika, a biyu ga watan Yuni za su je filin wasa na Red Bull Arena na garin Harrison na kasar Amurka.

Daga cikin adadin, akwai takwas masu taka leda a gida Najeriya.

’Yan wasan su ne kamar haka;

Masu tsaron raga: Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands); Adewale Adeyinka (Akwa United); Ojo Olorunleke (Enyimba International FC).

’Yan wasan baya: Olaoluwa Aina (Torino FC, Italy); Abdullahi Shehu (AC Omonia, Cyprus); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); William Ekong (Watford FC, England) Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); Isa Ali (Remo Stars); Chidozie Awaziem (Alanyaspor FC, Turkey); Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Calvin Bassey (Glasgow Rangers, Scotland); Ibrahim Buhari (Plateau United)

’Yan wasan tsakiya: Joseph Ayodele-Aribo (Glasgow Rangers, Scotland); Alex Iwobi (Everton FC, England); Oghenekaro Etebo (Watford FC, England) Chiamaka Madu (Rivers United); Babatunde Afeez Nosiru (Kwara United); Azubuike Okechukwu (Yeni Malatyaspor, Turkey); Samson Tijani (Red Bull Salzburg, Austria); Alhassan Yusuf (Royal Antwerp FC, Belgium)

’Yan wasan gaba: Ahmed Musa (Fatih Karagumruk, Turkey); Moses Simon (FC Nantes, France); Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain) Ademola Lookman (Leicester City, England); Sadiq Umar (UD Almeria, Spain); Emmanuel Dennis (Watford FC, England); Cyriel Dessers (Feyenoord FC); Victor Mbaoma (Enyimba FC); Ishaq Rafiu (Rivers United)