✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan ‘Alhajin Shagali’ ya daga darajarmu – Matar Marigayi Muhammadu

A makon da ya gabata ne Allah Ya yi wa shahararren dan wasan kwaikawayo nan wanda ke fitowa a shirin Gidan Kashe Ahu da aka…

A makon da ya gabata ne Allah Ya yi wa shahararren dan wasan kwaikawayo nan wanda ke fitowa a shirin Gidan Kashe Ahu da aka rika gabatarwa a tashar talabijin ta NTA Kaduna shekarun baya  Alhaji Muhammadu Abdullahi, kuma ana yi masa lakabi da Baba Dogara ko kuma Alhajin Shagali rasuwa, Aminiya ta ziyarci gidansa da ke kallon kofar Arewa ta Jami’ar Amadu Bello, Samaru Zariya, inda ya tattauna da daya daga cikin matansa, wadda suka kwashe tsawon shekaru talatin da biyar suna tare. Ta bayyana yadda suka yi rayuwa da mai gidanta, irin halayensa da sauransu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Da farko ko za ki gabatar da kanki a takaice?

Da farko dai sunana Hajiya Rabi’atu Ibirahim kuma ni ce Shugabar Makarantar Sakandaren Mata ta Giwa (principal GGSS Giwa) kuma ni ce matarsa ta biyu. Shekararmu talatin da biyar muna tare da shi cikin aure, kamar yadda ka ji, ko ka gani.

Shi fa Baban Tumbuleke?

Shi mai gidan namu ma’aikaci ne a Jam’iar Ahmadu Bello Zariya amman sai dai shi yana cibiyarsu da ke Ma’aikatar Kula da Dabbobi da ke Mando Kaduna. Shi mai gidanmu, matum ne mai son al’umma, mai kuma son al’umma su ji dadi. Mutum ne kuma mai yawan kyauta kuma mai yawan barkwanci. Yana son raha da son wasa da mutane, domin haka ne ma mutane suke kiransa da lakanin ‘Alhajin Shagali’ saboda yana da matukar son jama’a su yi shagali ne, su ji dadi. To, irin halayyar mai gidanmu ke nan.

To, ta yaya aka yi ya rika fitowa a wasan kwaikwayo a talabijin, ko shi ma ma’aikacin NTA Kaduna ne?

Mai gidanmu ba ma’aikacin gidan talabijin ba ne, sai dai yana fitowa a wani shiri da ake gabatarwa na Gidan Kashe Ahu. Kuma a lokacin da ya fara wannan shirin, a matsayinmu na mata sai muka fara kishi a zuciyarmu. Wato ba mu jin dadi amma da muka ga ya fara karbuwa kuma jama’a na son shirin kuma sai muka gane cewa ashe manufar shirin shi ne a fahimtar da al’umma sannan kuma a wayar masu da kai. Don haka sai muka daina kishi kuma har kosawa muke mu ga an gabatar da shirin a talabijin saboda yadda al’umma suke kallonmu, suke daukar mu da matsayi na musamman. Ba ma shi ba da yake shirin, har mu iyalansa jama’a so suke su ganinmu, domin wannan fita da yake yi a shirin ya daukaka darajarsa kuma mu ma ya daukaka tamu. Don haka aikin yada labarai kowane iri ne muke giramama shi, domin ta nan ake sanin mutum a duk inda ba ka zato kuma yanzu haka daya daga cikin ’ya’yana mace, ita ma tana aiki da kafafen watsa labarai saboda muhimmancin aikin da son shi da muke a zuciyarmu; a sanadiyyar shigar mai gidanmu cikin harkar kuma ya kara mana son al’umma.

Ko yaushe ya rasu?

Maigidanmu, Alhajin Shagali ya rasu yana dan shekara 73 da haihuwa kuma ya bar mata biyu da yara 13 tare da jikoki. Allah Ya jikansa da rahama, babu shakka mun ji dadin zama da shi.