✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wannan Sabuwar Shekara 01

Godiya, yabo da daukaka sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda ta wurin alherinSa yau muna cikin wadanda suke raye, a lokaci kamar wannan. Duk…

Godiya, yabo da daukaka sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda ta wurin alherinSa yau muna cikin wadanda suke raye, a lokaci kamar wannan. Duk mai tunani yakan zauna ya yi tunani game da rayuwarsa; ya kuma iya yin wadansu muhimman tambayoyi ga kansa. Ba wani sirri ba ne ko kadan mutum ya san cewa, kowace sa’a da ta wuce, sashin rayuwarmu a wannan duniya ya wuce, ba za mu kuma taba samun wancan zarafi ba, ko kadan sai dai wani sabo. Shi ya sa duk lokacin da muka ga rana ta fito; dole ga kowane mutum mai azanci ya yi shirin abin da zai yi domin cika nufin Allah cikin rayuwarsa. Kowace rana AMANA ce daga wurin Allah domin mu aikata nufinSa. Lokacin da ka kwanta da dare, ka kuma yi barci bambancinka da wanda ya mutu kadan ne kawai, watakila numfashin da kake yi ne kawai, domin ba ka san abin da ke aukuwa kewaye da kai ba, sa’anda kake barci. Amma idan gari na wayewa sai ka ga kanka cikin masu rai. Yawancin lokaci ba ma yin tunani cewa wadansu mutane sun kwanta tare da mu lafiyarrsu kalau babu labarin ciwo a jikinsu; amma ba su iya ganin hasken safiya ba, sun mutu – Allah Ya yi musu rasuwa kamar yadda muka saba fadi- Allah jikan rai- sai ga ka nan ka tashi daga barci lafiya, har ma kana neman dumamen karya kumallo. Mu sani fa babu dan Adam da yake da iko bisa ransa koda rabin dakika ne. Dole ne mu gane cewa dukanmu muna morar alherin Allah ne da Ya yarda Ya bar mu cikin masu rai.
A cikin tunanina – tambaya ta farko da ta shigo mini cikin tunani ita ce – Shin, me ya sa Allah Ya bar ni a cikin masu rai a yau? Muna lokaci ne da mutane da yawa ba sa yin tunanin yadda za su yi rayuwarsu ta yau da kullum domin ba su damu da ko me Allah Yake shiri game da rayuwarsu ba, kuma ba su kula su sani ba. A cikin shekarar da ta gabata wato 2013, na sani ka san mutane da yawa da suka mutu, ko kuwa suka shiga cikin wani mawuyacin hali. Wasu ma abokanka ne, kun kwana da su mai yiwuwa cikin daki daya, amma a yau sun riga mu gidan gaskiya. Wasu da yawa suna da kyakkyawan shiri domin kyautata rayuwarsu cikin shekarar da muka shiga amma duk da wancan shiri a yau ba sa cikin duniya, mai yiwuwa sun yi rashin lafiya sai ya zama sanadin cikawarsu. Wasu kuwa watakila cikin wani irin hadari ne suka rasa nasu ran, mai yiwuwa ne kana daya daga cikin wadanda suka yi hadari amma Allah cikin alherinSa Ya sa ka rayu. Shi ya sa ka iya ganin wannan sabuwar shekara cikin masu rai. Ko ka taba tambayar kanka mene ne ya sa ba ka mutu tare da sauran mutane da yawa da suka mutu ba? Ka yi tafiye-tafiye da dama zuwa wurare daban-daban a kan hanyar da wasu suka yi tafiya amma ba su dawo ba, sai ga shi kana nan cikin lafiya. A ganinka babu dalili ne?
Idan ka duba a hankali, mutane suna da shiri iri-iri, idan ka bincika kuma duk shirin da suke da shi shiri ne domin kansu kawai. Misali – an  rigaya an soma maganar siyasa a wannan kasa tamu wadda take zuwa kusan shekara biyu nan gaba. Wadansu ’yan siyasar sun yi alkawuran da suka saba yi, har ma wasu daga cikinsu su soma yin fada a cikin jam’iyyunsu a kan inda suke so su yi takara, kamar yadda suka saba, sun soma dadin baki. A yanzu haka; ita ce kawai tunanin irin wadannan mutane, Wasu kuwa suna tunanin yin kasuwanci ne, inda za su samu jari ko inda za su zuba jari. Wasu kuma suna tunanin yadda za su kashe wani ‘makiyinsu’ ko wanda aganinsu shi ya hana musu cika burinsu a cikin rayuwa. Kai fa mene ne naka shirin?  
Idan aka binciki cikin zuciyarka mene ne za a gani shi ne kudirinka a cikin wannan shekara? Yawancin lokaci mutane kalilan ne suke tunawa da Allah yayin da suke yin shirin wani abin da za su yi.
Sai ka tuna fa cewa ba kai ba ne kake rike da ranka, Allah Shi ne Mai komai Mai kowa. Kada ka yi kuskure irin na mutumin da Yesu Kiristi ya ce da shi wawa a cikin Littafin Luka 12: 15 – 21 inda yake cewa “Ya kuma ce musu, “Ku yi lura, ku tsare kanku daga dukan kyashi; gama ba da yalwar dukiya da mutum yake da ita ransa yake tsayawa ba. Ya kuma yi musu misali, ya ce, kasar wani mawadaci ta ba da da amfani da yawa; shi ma ya yi tunani a cikin ransa, ya ce, “Me zan yi, gama ba ni da inda zan tattara anfanina? Ya ce, “Abin da zan yi ke nan: in rushe rumbunana, in gina wadanda suka fi su girma; nan zan ajiye hatsina da wadatata duka. In ce wa raina kuma, Ya raina, kana da wadata mai yawa ajiye da za ta kai shekaru da yawa; yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa. Amma Allah Ya ce masa, KAI WAWA, yau da daren nan ana bidar ranka a gare ka, abin da ka shirya fa ga wa suke? Haka nan ne mai ajiye wa kansa dukiya, shi kuwa ba mawadaci ba ne ga Allah.”
Idan muka yi binciken wannan wuri a hankali, za mu ga cewa; mutane da yawa a zamaninmu suna da hali irin wannan. Halin kyashi ya cika zuciyar mutane da yawa, son kai da mugunta, su suka mamaye zukatan mutane, kansu ne kawai suka sani; kowane abu mai kyau suna so ya zama nasu; idan suka samu, ba sa iya taimakon wadanda suke kewaye da su. Yesu Kiristi ya ce wauta ce ga kowane mutum da shi sai kansa ne kawai ya sani. Mai yiwuwa haka kake rayuwarka tun da, ba ka kula da kowa ba sai kanka, to bari ka sake duba karshen irin wannan mutane – kai wawa, yau da daren nan ana bidar ranka a gare ka, abin da ka shirya fa ga wasu ke nan? Shi ne abin da kake so ka ji lokacin da kwanakinka suka kare a wannan duniya? Idan har ba ka so ka zama wawa a gaban Allah; to dole sai ka soma sa Allah cikin dukan shirin da kake yi.
Addu’ata dominka ita ce, a cikin wannan sabuwar shekara, ba za ka zama wawa ba, Yanzu ne ya kamata ka nemi nufin Allah game da ayyukanka na wannan shekara, ka tambayi Allah cikin addu’a domin Ya fahimtar da kai game da abin Yake so ka yi maSa. Akwai shirinSa domin kowane dayanmu, mu dauki zarafi cikin addu’a watakila har da azumi domin mu san su. Kada mu zama wawaye!
Ubangiji Allah Ya taimake mu.