✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wannan karon ba sanyi a mulki – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin aiki babu kama hannun yaro a zangon mulkinsa na biyu wajen magance matsalolin da kasar nan ke…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin aiki babu kama hannun yaro a zangon mulkinsa na biyu wajen magance matsalolin da kasar nan ke fuskanta.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) ta kai masa ziyara a Fadar Shugaban Kasa a Abuja, inda ya ce ba zai ba ’yan Najeriya kunya ba.

Shugaba Buhari ya ce, “Wannan shi ne zangon mulkina na karshe, don haka zan kara kaimi fiye da yadda na yi a da. Ina tabbatar muku cewa ba zan ba ku kunya ba. Zan yi iya kokarina, sannan  zan yi addu’a domin kokarin nawa ya yi amfani.”

Da yake kara bayani kan yadda na’urar tantance masu kada kuri’a ta taimaka a zaben 2015, Shugaba Buhari ya ce lokacin da ake zama a rubuta sakamakon zabe ya wuce.

“Sau uku ana kada ni a zabe, sannan na shigar da kara a kotu har na je Kotun Koli sau uku, amma duk da haka abin bai yiwu ba. Amma da taimakon Allah da taimakon kimiyyar zamani, sai ga shi na samu nasara. Ta hanyar amfani da katin zabe na dindindin, ya zama dole a kirga kuri’un talakawan Najeriya,” inji shi.

Ya ce “Kun san a da can zama kawai ake yi a rubuta sakamakon zabe, sannan a ce wanda bai amince ba ya tafi kotu. Mutumin da ke neman na abinci ina zai iya daukar manyan lauyoyi ya shigar da kara? Amma da yake Allah Yana da hanyoyin da Yake amfani da su wajen magance matsala, sai Ya yi ikonSa, don haka muna yi maSa godiya bisa fasahar da Ya ba mu.”