✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa dan acaba yankan rago a Legas

Wani wanda ya yi wa dan acaba yankan rago, ya kuma tsere da mashin dinsa, ya gurfana a gaban wata Babbar Kotun Majistare a Jihar…

Wani mutum ya gurfana a gaban alkali a bisa zargin kisan wani dan acaba ta hanyar yi masa yankan rago.

Baya ga zargin kisa ana kuma tahumar shi da yi wa wani mutum daban fashin babur ta hanyar amfani da wuka.

An dai gurfanar da wanda ake zargin ne a Babbar Kotun Majistare da ke Ebute Meta a Jihar Legas.

A cewar mai gabatar da kara, ASP Julius Babatope, wanda ake zargin ya aikata laifin ne unguwar Agbowa da ke wajen garin Legas a ranar 30 ga watan Yuni.

Ya shaida wa kotun cewa mutumin ya zo wurin wani mai sana’ar acaba mai suna Sanni, ya kuma nemi ya kai shi wani wuri.

Suna cikin tafiya sai Yezidu ya zaro wuka yanke shi a wuya, sannan ya gudu da babur din mamacin.

Bugu da kari, wanda ake zargin ya tsare wani Mista Adeyemi da wuka, ya kuma kwace mishi babubr kirar Bajaj da kudinsa ya kai Naira 365,000.

Wanda ake zargin ya amsa tuhumar da aka yi masa na fashin babur, amma kuma ya bai ce komai ba a tuhumar kisan kai.

Alkalin kotun, Mai shari’a Misis M. Ajayi ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Ikoyi.