✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani sojan bogi ya shiga hannun sojoji a Jos

Rundunar Sojin Operation Safe Haven (OPSH), ta kama wani mutum da yake gabatar da kansa a matsayin jami’inta. An kama shi ne tare da wani…

Rundunar Sojin Operation Safe Haven (OPSH), ta kama wani mutum da yake gabatar da kansa a matsayin jami’inta.

An kama shi ne tare da wani wanda ya kware wajen yin katin shaidan jabu na jami’an tsaro.

Rundunar ta kuma kama wasu mutane 20 da shekarunsu ke tsakanin 20 zuwa 25 da laifukansu suka hada da fashi da makami da shaye-shaye da satar wayoyin hannu da sauran laifuka.

Kwamandan Rundunar, Manjo Janar Chukwuemeka Okonkwo, da ya gabatar da masu laifin ranar Lahadi ya ce an kama su ne a wurare daban-daban a cikin garin Jos, babban birnin Jihar.

Okonkwo ya sun kama su ne a yunkurin tsare garin na Jos daga kanana da manyan laifuka domin samun dorewar zaman lafiya.

“A kokarin zakulo bata-gari, dakarunmu sun kamo miyagun muatnen da ke hana garin Jos zaman lafiya.

“Daga cikinsu akwai sojan bogi, da mai yin katin shaidan jabu na jami’an tsaro. Sai kuma wasu mutane 20 da aka kama za mu mika su wajen ‘yan sanda domin a kai su kotu ta yanke musu hukunci”, inji shi.

Ya kuma tabbatar wa mazauna garin Jos cewar za su yi iya kokarin ganin sun yi waje da duk wasu miyagin mutane don kawo karshen rashin zaman lafiya a jihar.