Jama’a sun yi ta guje-guje a cikin dare, suka kuma kwana cikin zullumi a garin Geidam na Jihar Yobe, bayan jin fashewar wasu abubuwa masu karfin gaske.
Jin wannan kara mai karfi ya haifar da fargabar yiwuwar kai hari daga mayakan kungiyar Boko Haram/ISWAP a tsakanin mazauna gari, wanda shi ne hedikwatar Karamar Hukumar Geidam.
- ISWAP ta kai hari Chibok ta sace ’yan mata
- Dalilan Da Buhari Zai Yi Kidayar Jama’a a yanayin rashin tsaro
Wani mazaunin garin da ya bukaci Aminiya ta sakaya sunansa ya bayyana cewa “Mun ji wasu kararraki da suka sa muka garzaya gida muka kulle kofofinmu, muna zaune cikin firgici kuma ba mu san ainihin abin da ke faruwa a yanzu ba.”
Aminiya ta tuntuni Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, wanda ya shaida wa wakilinmu cewa kokarin sanin hakikanin halin da ake ciki a garin na Geidam, da zarar sun tabbatar da hakikanin bin da ya faru zai sanar.
Garin na Geidam dai yana gab ne da kan iyaka da garin Maine Sarua na Jumhuriyar Nijar, inda akan fuskanci hare-haren mayakan Boko Haram.
Irin wannan lamarin dai kan sa al’ummar garin guje-guje domin tsira da rayukansu.