Wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wane ne ba ya kashe kansa ta hanyar rataya a Jihar Bayelsa.
Lamarin dai ya auku ne a ranar Lahadi a gadar saman da ke daura da gidan mai na NNPC da ke kan titin Sani Abacha a Yenagoa, babban birnin jihar,
- Gwamnati ta shawarci ’yan Najeriya masu zuwa Amurka da Ingila su yi hankali da barayi
- Ban ga laifin masu barin Najeriya don neman ingantacciyar rayuwa ba – Kakakin Buhari
Yanayin rayuwa ya yi tsauri a Jihar Bayelsa bayan da ambaliyar ruwa ta yi kamari a baya da ta yi illa ga rayuwar mazauna jihar.
Mutane da dama sun rasa hanyar samun kula da kansu sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan.
Aminiya ta binciko cewa masu bibiyar hanyar ce suka gano gawar marigayin a kan gadar saman a ranar Lahadi.
Yayin da wasu mazauna garin ke ganin cewa marigayin mahaukaci ne, wasu kuma na cewa ya kashe kansa ne saboda kuncin rayuwa.
Wata mazauniyar yankin mai suna Mercy Didi, ta ce an saba ganin mamacin a kasuwar Swali da ke yankin kafin rasuwarsa.
Ta ce: “Amma ban sani ba ko mahaukaci ne. Amma abin da na sani shi ne ba na kallonsa a matsayin mahaukaci.”
Wani mazaunin garin, Luke Armstrong, ya ce tabbas ya rataye kansa ne saboda bacin rai, saboda yanayin rayuwa a Najeriya.
Ya ce: “Rayuwa ta yi wuya a yanzu, ko a jihar nan, abubuwa sun yi wuya, kowa ta kansa yake yi. Amma duk da haka bai kamata mutum ya kashe kansa ba.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an killace gawar mamacin dakin ajiye gawarwaki na Babban Asibitin Tarayya, yayin da ake ci gaba da gudanar bincike.