Wani mutum mai suna Dedoon ya kashe matarsa da duka a kauyen Adekaa da ke garin Gboko a cikin Karamar Hukumar Gboko da ke cikin Jihar Benuwe.
Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, Moses Joel Yamu, ya ce mutumin ya kashe matarsa ne ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe uku da rabi na dare a gidansu da ke kan titin Joseph Tiah a yankin Gboko ta Arewa sannan ya gudu.
“Lokacin da ’yan sanda suka halarci wurin sun dauki gawarta zuwa asibiti inda aka tabbatar ta mutu sannan kuma sun dauki jininta da ya zuba da wani gatari da mijin ya yi amfani da shi wurin kisan”. Inji Yamu
Mai Magana da Yawun Rundunar ’yan sandan jihar ya bayyana cewa ’yan sanda suna ci gaba kokarin kamowa tare da gurfanar da shi a gaban shari’a.
Aminiya ta gano cewa mijin ya kulle kofar dakin da suke ciki inda ya rika dukan matar tasa har sai da ta mutu daga bisani kuma ya haura ta tagar dakin ya gudu.