✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya kamu da cutar Kyandar Biri a Landan bayan ya ziyarci Najeriya

Ya kamu da cutar ne bayan balaguro zuwa Najeriya da ke Yammacin Afrika.

Hukumomin lafiya a Ingila sun ce an samu wani mutum da gwaji ya tabbatar da ya kamu da cutar kyandar biri da ba a saba gani ba a kasar.

BBC ya ruwaito hukumomin kasar suna cewa ya kamu da cutar ne bayan balaguro zuwa Najeriya da ke Yammacin Afrika.

A cikin wata sanarwa Hukumar lafiya ta Birtaniya (UKHSA) ta ce ana kula da lafiyar mutumin a hannun kwararru a bangaren cututtka masu yaduwa a asibitin Guy’s and St Thomas’ NHS Foundation Trust a Landan.

“Yana da mahimmanci a jaddada cewa cutar kyandar biri ba ta saurin yaduwa tsakanin mutane kuma hadarin yada cutar ba ya da girma, ”in ji babban jami’in asibitin ta UKHSA Colin Brown.

Kyandar biri da ake kira Monkey pox cuta ce mai yaduwa da aka kawar da ita a shekarar 1980.