✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani matashi ya auri mata biyu rana daya a Jos

Wani matashi kuma jigo a Jam’iyyar PDP, sannan Ko’odinetan PDP N-YES na Kasa, Alhaji Kabiru Muhammad Garkuwa ya ba jama’a mamaki lokacin da ya agwance…

Wani matashi kuma jigo a Jam’iyyar PDP, sannan Ko’odinetan PDP N-YES na Kasa, Alhaji Kabiru Muhammad Garkuwa ya ba jama’a mamaki lokacin da ya agwance da ’yan mata biyu a garin Jos fadar Jihar Filato a ranar Asabar da ta gabata.

Auren biyu an daura su ne a Masallacin Kan Tudu, ’Yan Tifa da ke Abba Na-Shehu a tsakaninsa da Maryam Umar Muhammad da kuma wanda aka daura a tsakaninsa da Jamila Musa Ibrahim a Masallacin Kofar Gidan Alhaji Bala Maibodi da ke Titin Salisu Tabacco, dukkansu a garin Jos.

Kafar labarai ta Legit.ng ta ruwaito wani abokin angon yana cewa an daura auren ne bisa bambancin minti biyar, sai dai katin gayyatar dauren auren biyu da Aminiya ta samu a shafin Facebook din angon, ya nuna an shirya daura aurensa da Maryam ne da misalin karfe 11 na safe, yayin da aka shirya daura aurensa da Jamila da misalin karfe 2:00 na rana. Kuma da Aminiya ta tuntubi angon ta wayarsa ya tabbatar da cewa an daura auren ne kamar yadda aka nuna a katin gayyatar, wato karfe 11:00 na safe da karfe 2:00 na rana.

Ango Kabiru Muhammad Garkuwa ya shaida wa Aminiya cewa ba wannan ne aurensa na farko ba, amma amaren biyu ’yan mata ne da wannan ne aurensu na farko.

Auren mace fiye da daya a lokaci guda abu ne da ba a cika samunsa ba duk da cewa addinin Musulunci ya amince namiji ya auri mace guda zuwa mata hudu idan yana da hali da ikon da zai tabbatar da adalci a tsakaninsu.

Tuni aminai da abokan angon suka rika aikewa da sakonnin taya murna da fatar alheri ga angon da amaren a shafukansu na kafafen sadarwar zamani musamman facebook.

Misali Aminu Yousouf Mai Maggi cewa ya yi: “Kai! Allah Ya ba da zaman lafiya.” Yayin da Umar Tijjani ya ce: “Amin, namijin duniya!”Shi kuwa Yusuf Umar cewa ya yi: “Allah Ya ba da zaman lafiya.” Sai kuma Junaid Rabiu ya ce: “Ka ji namijin gaske!” Ambasada Maizaleka Malam Madori kuwa cewa ya yi: “Congratulations Kabir Muhammad Garkuwa.” Sai Rondong Wash Pam ya ce, “Congratulations my brother.” Emmanuel Loman kuma ya ce, “Big congratulations!”

Haka dai jama’a suka rika aikewa da sakonnin taya murna ga angon amare biyun.